A JIYA Asabar Allah ya ɗauki ran babban ɗan kasuwar finafinan Hausa ɗin nan da ke Kano, Alhaji Nasiru Dararrafe.
Ya rasu da safe a wani asibiti mai zaman kansa a Kano bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Marigayin, mai shekaru 55, ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya 26.
Alhaji Nasiru Dararrafe babban ɗan kasuwar finafinan Hausa ne a lokacin ana kasuwancin kaset da sidi.
Yana a sahun gaba har duniya ta san shi a wannan harkar.
Bayan harkar kasuwancin kasasuwa da sidi ɗin bidiyo ta mutu, Dararrafe ya koma saida bulawus inda a nan ma ya yi fice kuma ya ci gaba da harkar har zuwa lokacin da Allah ya karɓi rayuwar sa.
Allah ya jiƙan sa, ya kyautata makwancin sa.