WASU ɓarayi masu garkuwa da mutane (kidinafas) sun bayyana cewa sai an biya diyyar dalar Amurka wuri na gugar wuri har 100,000 kafin su sako wasu ‘yan fim na Nijeriya da su ka kama.
‘Yan fim ɗin dai su ne jaruman masana’antar shirya finafinai ta Nollywood guda biyu, wato Cynthia Okereke da Clemson Cornel, wanda aka fi sani da laƙabin Agbogidi.
Shugaban Ƙungiyar Jaruman Fim ta Nijeriya, wato ‘Actors Guild of Nigeria’ (AGN) na ƙasa, Ejezie Emeka Rollas, ya bayyana cewa ɓarayin sun tuntuɓi iyalan jaruman har su ka buƙaci biyan wannan diyyar ta $100,000.
Ya ce iyalan jaruman ne su ka fara bada sanarwar cewa ‘yan wasan, waɗanda membobin ƙungiyar sa ne, sun ɓace bayan da su ka halarci wajen ɗaukar wani fim a garin Ozalla da ke Jihar Inugu.
Rollas ya ce su na nan su na addu’a ga Allah da ya saka hannu cikin wannan lamarin kuma ya kawo farraƙa a cikin ɓarayin.
Rollas ya ƙara da cewa, “Mu na nan kuma mu na aiki tare da jami’an tsaro daban-daban domin a samu a sako ‘yan wasan, amma kuma ba mu da tabbacin abin da za su bijiro mana da shi domin irin wannan lamarin ya na faruwa a ko’ina a ƙasar nan.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a yanzu dai Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Inugu ta shiga cikin zancen, har ta baza komar ta domin gano inda ake tsare da jaruman tare da kama ɓarayin.
Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, DSP Daniel Ndukwe, ya bada sanarwa a ranar Asabar cewa, “Mu na da rahoto da ya shafi wata mota da aka gani a yashe, mun ɗauko ta, da kuma batun wata mace da ta ɓata.”
Ya ce an samu motar ne a wurin da ake kira ‘Four-Corners’ da ke babbar hanyar Inugu zuwa Fatakwal, a daidai ƙauyen Ozalla da ke cikin Ƙaramar Hukumar Nkanu West ta Jihar Inugu.
Ya ce: “A ranar 29 ga Yuli, wajen ƙarfe 7:30 na safe, mu ka samu labarin cewa an ga wata mota mai launin ja, ƙirar Toyota RAV4 Jeep mai lamba AGL 199 CY an yi fakin ɗin ta da alamar an bar ta, a bakin hanya a ‘Four-Corners’ da ke babbar hanyar Inugu zuwa Fatakwal.
“Daga nan, an ziyarci wurin an ɗauko motar.
“Kamar arashi, da misalin ƙarfe 11:30 na safe kuma a wannan ranar dai, aka kawo rahoton cewa motar ta wata mai suna Cynthia Okereke (mace) ce, ‘yar wasan Nollywood, wadda rabon da a gan ta tun ranar 26 ga Yuli.”
Kakakin ‘yan sandan ya ce rahoton da rundunar ta samu ya nuna cewa mutum ɗaya ne kaɗai aka ce ya ɓace.
Sai dai Daraktar Yaɗa Labarai ta Ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya, Misis Monalisa Chinda-Coker, ta ce iyalan jaruma Okereke da jarumi Clenson Cornel sun bada tabbacin ba su dawo gida ba tun da su ka bar lokeshin ɗin shirya fim a ƙauyen Ozalla.
Chinda-Coker ta faɗa a wata sanarwa cewa: “Membobin biyu na Ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya, Okereke da Cornel mai laƙabi da Agbogidi, ana kyautata zaton sun ɓata bayan iyalan gidajen su sun bada tabbacin cewa ba su dawo daga lokeshin ɗin fim a ƙauyen Ozalla ba.
“Ana zargin cewa an sace membobin guda biyu kuma wannan ya ƙara haifar da fargaba a zukatan ‘ya’yan ƙungiya dangane da tsaron lafiyar ‘yan wasa masu ɗaukar fim a ƙasar nan.”
![]()






