Tabbas zai kai. Don a 1971 ya biya mani allo na a makarantar Malam Baba Ɗan Malam Hasan. Da ka ya biya mani. Na yi ta mamaki ina yaro ɗan shekara 10, wai ga wani ya haddace Ƙur’ani. Yau ni ma ina da shekara 63 a ƙirgen Hijira, 61 a ƙirgen Turawa… To ina ya shi?
Amini ne ga mahaifi na. Allah ya jikan sa.
Sai dai na gagara zama Shehu duk da na yi burin zama haka ina yaro. Sai na ɓige da zama riƙaƙƙen ɗan boko.
Wannan na ke nufi a wata ƙasida ta (هاءية اللغة العربية) da na gabatar a gaban malaman Larabci na manyan makarantun Nijeriya da su ka gayyace ni shekarun baya:
تمنى الفتى أن يكن طالبا — ليصبح يوما يعلمهافأحظى الإله له غيرها — أتاه المشيب بلا علمها
Ina ruwan rigima Ltd! Kai da aka gayyata ka ba da jawabin baƙo mai jawabi, sai ka rubuto jawabin a ƙasidance gaban malaman Larabci?
Allah ya ƙara wa Shehu Ɗahiru Usman Bauchi lafiya da tsawon shekaru masu amfani.
* Dakta Aliyu U. Tilde shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi
![]()







