ƊAYYAB Abdulrazak, wanda aka fi sani da Olatunji a harkar waƙa, ya na ɗaya daga cikin mawaƙa da su ka yi tashe a Jihar Kaduna a shekarun baya, musamman a lokacin wata waƙar sa mai suna ‘Karabayye’.
Mujallar Fim ta taɓa yin hira da shi a shekarun baya, inda ya bayyana tarihin sa da yadda aka yi ya fara waƙa, da sauran su.
A wannan karon, wakilin mu ya nemi Olatunji don jin halin da ya ke ciki game da harkar waƙa, kasancewar an daina jin ɗuriyar sa a masana’antar a tsawon lokaci. Mawaƙin ya amsa dukkan tambayoyin da aka yi masa, har da batun matsalar da aka ce sun samu shi da fitaccen mawaƙi Naziru Sarkin Waƙa a kan waƙar ‘Karabayye’.
FIM: An daɗe ba a jin ɗuriyar ka a fagen waƙa ba. Ina ka shige ne?
ƊAYYAB OLATUNJI: Alhamdu lillahi. Shi lamari na harkar waƙa ba wai na yi shiru ba ne, abu ne wanda ƙaddara na ɗaukaka ko na rashin ɗaukaka ya na hannun Allah ne: yadda ya ba ka dama ka buɗa haka za ka zama, yadda kuma ya ba ka rauni a kan lamari haka za ka zama.
Tun daga wancan lokacin ban daina waƙa ba, har yanzu ina yi, amma ka san lamari na rayuwa sai ka tsinci kan ka ga abin da ka ke so ka yi sai ya gagare ka. To amma zuwa yanzu alhamdu lillah na samu nasarori, saboda na daɗa samun wasu luɗufin da na sa harkoki na a hanya domin samun cigaba da samun hasken ɗaukaka na a kan harka ta waƙa.
FIM: A yanzu da aka fara harkokin siyasa, ko ka na da ɗan takara, musamman ganin lamuran sun canza, an koma tafiya a ƙungiyance, saɓanin a baya da mutum ke harkar sa shi kaɗai?
OLATUNJI: Ka san mu mawaƙa kamar bishiya ne, mu na da rassa kala-kala. A siyasance, duk wanda ya kira mu ya nemi ya yi tafiya tare da mu mu na maraba da shi, domin ɗan ƙasa ne, ɗan Nijeriya ne, a yadda ya neme mu haka za mu bi shi. Amma akasari waɗanda su ka neme mu su ka yi mana riƙon ɗa da uba mun fi karkata a wannan. Haka kuma mu kan kalli ƙasar, wane irin mutum ta ke buƙata. In mu ka dubi wanda ta ke buƙata kuma jajirtacce, mu kan ɗan karkata wurin bin sa a kan sauran ‘yan takarkarun.

A yanzu gaskiya akwai ƙungiya da mu ke kiran ta ‘Gida-Gida’. Wannan ƙungiya ita mu ke bi daga sama har zuwa ƙasa, kuma jam’iyyar da mu ke ita ke jan ragamar ƙasar, a halin yanzu wannan jam’iyya mu ke bi.
FIM: Kai ma ka bi wannan tsari na tafiya a ƙungiyance kenan?
OLATUNJI: Gaskiya ne, a ƙasashen duniya ƙungiyoyi ne ke samun nasarori. In ku na da ƙungiya an fi karɓan ku a mutunce, sannan me ku ke yi, an san yawan ‘ya’yan ku da shugabannin ku, ga ta nan ne idan abu ya samu da ku ne za a yi. Ka ga kuma babu ta yadda wani zai zo ya yi amfani da ku daga baya ya kwanta a kan ku ya amfana. In ku na da ƙungiya babu wanda zai yi maku wannan. Wannan ya sa mu ka ga ƙungiya ta na da muhimmanci, dole mu yi ta.
FIM: A wasu lokuta a baya an yi ta magana a kan cewa kun samu matsala kai da Naziru Sarkin Waƙa. Mecece gaskiyar maganar?
OLATUNJI: To, ka san ita rayuwa, kamar yadda al’umma su ke ta yaɗa waɗannan maganganu tsakani na da Naziru, magana ne na in arziki ya zo maka sai ka fara samun hassada da kuma waɗanda su ke ganin ba kai ne ka dace ka samu wannan arzikin ba.
Ni, Ɗayyab Abdulrazak Olatunji, tsakani na da Naziru kyakkyawar fahimta ce ba tun yau ba, tun a baya ya fahimce ni, na fahimce shi. Abin da na sani shi ne shi da kan sa ya kira ni ya ce, “Duk wanda ya zo maka da labari na ka ɗauke shi munafikin mu. Haka ni ma duk wanda ya zo min da labarin ka na ɗauke shi munafikin mu.” Wannan ya sa mu ka ɗinke, aka rasa gane kan yadda mahassadan su ke so su fahimci Olatunji a ƙasa ya ke ko ya faɗi ko kuma da sauran sa har yanzu. Allah ya rufa wannan asiri, kuma har abada, in-sha Allahu.
FIM: Amma kuma an ce a kan wata waƙar sa ce mai suna ‘Karabayye’ da ka ke amfani da ita a matsayin taka. Domin a wancan lokacin ana ɗaukar waƙar a matsayin kai ka rera ta, kuma kusan ita ce waƙar da ta fito da kai. To kuma an ce saboda ka na amfana da waƙar, wannan ya sa shi kuma ya dakatar da kai. Haka ne?
OLATUNJI: To haka jama’a su ka ce. Shi dai Naziru ya san wanene Olatunji, kuma ni ma na san waye Naziru. Shi kuma wannan maganar jama’a ne ke ta surutu a kan wannan don neman biyan wasu buƙatun su ko don neman sanin wani abu. Amma tsakani na da Naziru mu mu ka bar wa kan mu sani, don haka wannan magana sirri ne tsakani na da shi, shi ya sa yanzu ba zan iya cewa komai a kan wannan magana ba.
FIM: Kasancewar waƙoƙin yanzu sun bambanta da na da, ko kai ma ka bi sahun mawaƙan wannan zamani don bin sahun su?
OLATUNJI: Gaskiya ne, waƙa ta zamani babu yadda ba za ka sarrafa shi ba; za ka iya ɗaukar waƙoƙin da kuma sarrafa su ka mai da su na zamani, kalaman ka su tsaftata yadda za su yi kama da na zamani. Akwai wata waƙa da na yi, ta marayu da na yi, kuma a yanzu haka jama’a na jin ta sosai. Wannan kuma ya faru ne dalilin maida ta na zamani da na yi. Ni yanzu kullum kalamai nan ake ta ƙoƙarin gyarawa. Shi ya sa na hau kan wannan tsari.
FIM: Kasancewar kasuwar finafinai da waƙoƙi ta mutu, a ina ka ke samun kuɗaɗen shiga?
OLATUNJI: Gaskiya idan na yi sababbin waƙoƙi ko a da sanin fuskar nan dai ke jawo min alkhairi, don mafi akasari ko jihar nan na bari na tafi wata jiha wurin wasu shugabanni za su ce kai mu na ganin ka, sai in ce na fahimci a inda ku ke gani na, daga nan sai ka ga abin da ban taɓa tsammani ba ma sun shigo hannu na. To, gaskiya ta nan ne ni na fi samu alkhairai na.

FIM: Akwai wani tsari da mawaƙan duniya ke amfani da shi yanzu, kuma har a nan Arewa mawaƙa na amfani da shi, wato ‘Audiomack da YouTube. Ko kai ma ka shiga wannan tsari?
OLATUNJI: E, gaskiya ina da sha’awar wannan, amma ban riga da na shiga wannan tsarin ba. Saboda shi lamari in za ka yi shi, ka riƙa dubawa ka na yi daidai rayuwar ka. A gani na, idan na shiga wannan a yanzu zai shiga hurumin kulawa da iyali na da kuma ainihin wasu abubuwa waɗanda ba a sahun waƙa su ke ba. Wannan ya san a ɗan tsahirta tukunna, in Allah ya taimake ni na ci ƙarfin wancan lamari, sai in zo in saka komai a kan tsari in Allah ya yarda.
FIM: Ina alaƙar ka da Adam A. Zango, wanda wasu na tunanin ba ku tare a yanzu?
OLATUNJI: Gaskiyar magana, Adam A. Zango mutum ne wanda ya ba ni gudunmawa, ya kuma taimaka min a lokacin da na ke yunƙurawa. Na jingina da shi domin na ƙara samun nasarori a dukkan lamari na, kuma bai ƙyamace ni ba. Mun ba juna gudunmawa. Amma ka san lamari na rayuwa, kamar yadda na faɗa maka, abu na iya zuwa maka ka tsinci kan ka a Kaduna ka koma Kano ko ka na Kano ka dawo Kaduna. So, abubuwa na ne su ka faɗaɗa, kuma haɗuwar mu ta yi wahala. Amma a gaskiyar magana, har abada ina tare da Adam A. Zango.
![]()







