HAFSAT Hassan, wadda aka fi sani da Amme, sabuwar jaruma ce da ta fara haskawarawar ta a masana’antar fim. Duk da yake ba ta daɗe da shigowa ba, amma har ta fara samun fice, musamman a waƙoƙin da su ke fitowa a wannan lokacin.
A cikin tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, jarumar ta bayyana yadda ta shigo harkar da yadda ta samu kan ta a ciki.
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
HAFSAT HASSAN (AMME): To, ni dai suna na Hafsat Hassan, wadda aka fi sani da Amme. Kuma ni haifaffiyar Maiduguri ce. Ina da shekaru 27. Na yi makaranta zuwa sakandare. Amma dai a Kano na yi rayuwa har na yi aure na haifi yara uku, daga baya kuma auren ya mutu, kuma yanzu ga shi na samu kai na a cikin harkar fim.

FIM: Yaya aka yi ki ka samu kan ki a cikin harkar fim?
AMME: Ka san duk abin da ya kasance ka na da rabo a ciki to sai ka same shi, don haka sai ya zama ina rayuwa a cikin ‘yan fim ta dalilin yaya na. To da haka har na zo na ji ina da sha’awar harkar.
FIM: Da wane fim ki ka fara kuma a wace shekarar?
AMME: Na fara yin fim ɗin ‘Uwar Gulma’ a cikin shekarar 2021. Kuma na yi waƙoƙi kamar guda biyar, sai kuma finafinan da na yi wanda zan fito kamar sin ɗaya sin biyu, sannan akwai finafinan barkwanci da ake sakawa a YouTube, da sauran su.
FIM: An ce ki na yin waƙoƙi na siyasa ma, ko?
AMME: Gaskiya ne ina yin waƙoƙin siyasa domin na yi wa mutane da dama, kuma ina kan yi ma a yanzu.
FIM: A yanzu an fara ganin fuskar ki ba kamar a baya ba. Ko yaya za ki kwatanta rayuwar ki ta baya da kuma a yanzu?
AMME: To rayuwa ta baya dai ina yin ta cikin sauƙi, amma a yanzu sai ya zama kowa ya na son ya yi magana da ni. To sai abin ya zame mini wani sabon abu, don yanzu duk inda na je sai a riƙa cewa, ‘Ai na gan ki a fim kaza’. To sai abin ya yi ta burge ni, ina son hakan, don haka wani lokacin ma idan zan je wani waje sai na saka abin rufe fuska, saboda idan mu ka je musamman wajen aiki sai ka ga yara su na zuwa su na so su yi hoto da mu. To, haka dai na ke rayuwar a yanzu. Kuma na samu abubuwa da dama, don sai ka je waje haka mutane su karɓi lambar ka su na son su yi magana da kai. Ka ga wannan sauyin rayuwa ne wanda a baya babu shi don ba kowa ya san ka ba.

FIM: Yanzu wane irin buri ki ke so ki cimma a harkar fim?
AMME: Gaskiya ina son na zama fitacciyar jaruma wadda za a riƙa yin alfahari da ita a wajen tallata abubuwan da su ka shafi al’adar mu ta Hausa da Kanuri.
FIM: Ko kin samu wata matsala a shigowar ki cikin harkar?
AMME: Gaskiya ban samu ba, tunda da man na faɗa maka ni ina da gata a cikin ‘yan fim, domin ko a yanzu ina alfahari da ubangida na, Sani Indomie, domin shi ya fara saka ni a fim. Kuma duk wata nasara da na samu, to shi ne ya tsaya mini. Don haka babu wata matsala da na samu.

FIM: Wanne saƙo ki ke da shi?
AMME: To, saƙo na dai ga masoya na shi ne kada su ga mu na harkar fim su riƙa ɗaukar mu ‘yan iska, karuwai. Don haka a daina yi mana waɗannan kalaman, domin kowane aiki da ka gani, akwai nagari akwai na banza; don haka ba mu taru mun zama ɗaya ba.
![]()






