• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 18, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cin zarafin ‘yan fim: Mu na goyon bayan Iyan-Tama, cewar MOPPAN

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 6, 2022
in Labarai
0
Malam Al-Amin Ciroma

Malam Al-Amin Ciroma

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta bayyana cewa ta na goyon bayan ƙarar da babban furodusa Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya kai wani mutum mai ɓata sunan ‘yan fim a Facebook.

Mujallar ta ruwaito a jiya cewa Iyan-Tama ta maka wani matashi mai suna Imam Aliyu Indabawa a Babbar Kotun Jihar Kano saboda cin zarafin sa da ya yi a wani rubutu da ya yi a Facebook tare da yun jama’u kan dukkan ‘yan Kannywood.

Kotu ta miƙa wa Indabawa da sammaci a jiya Litinin inda ta buƙace shi da ya bayyana a kotu don amsa zargin cin zarafi da ɓata suna.

A yayin da ya ke yin tsokacin uwar ƙungiyar ‘yan fim kan al’amarin, kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya faɗa wa mujallar Fim cewa, “Ɗaukar mataki a kan irin waɗannan mutane ɗaiɗaiku da kuma duk wata ƙungiya da ke cin mutunci da ɓatanci ga ‘yan fim a kan abin da ba su ji ba ba su gani ba shi ne abu mafi fifiko da mu ka sa a gaba.”

Ciroma, wanda darakta ne kuma jarumi, ya ƙara da cewa: “Misali, kowace ƙungiya da ta shigar da ƙara, MOPPAN za ta mara masu baya don ganin lallai an ƙwato masu haƙƙin su, haka nan kuma a ɗaiɗaikun su. Duk wanda ya yi irin wannan mu na goyon bayan sa don shi ne adalci.

“Ta ɗaya ɓangaren kuma, idan akwai wanda ya ke da matsala da wani ɗan fim, idan matsalar ta kai ba zai iya zuwa ga ƙungiya ya kawo ƙara ba, to ya kai ga hukuma, ya daina ɗaukar doka a hannun sa.

“A ɓangare na biyu kuma, masu shaci-faɗi, irin su su na nan da yawa, wanda babu abin da su ke so illa su samu ‘followers’ ko kuma su burge wasu mutanen da su ke so su burge. Waɗannan idan su na yi a da, to yanzu za su san cewa kan mu a haɗe ya ke, sai mun ƙwato wa kowa haƙƙin sa daidai gwargwado. 

“Mu ba hukuma ba ne, amma a ƙungiyance mu na da kyakkyawar alaƙa da dukkan hukumomi, kuma su na mara mana baya a kan dukkan wanda ya nemi ya ci zarafin ɗan fim ko ita masana’antar ko kuma kowacce daga cikin ƙungiyoyin ‘yan fim. 

“To wannan shi ne ra’ayin mu a kan dukkan mai neman ɓatanci ga ‘yan fim.”

Sai dai Ciroma bai fito ya bayyana irin mara wa Iyan-Tama bayan da za su yi ba.

Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa tun a watannin baya  Iyan-Tama ya sanar da Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, da shugaban ƙungiyar ‘yan fim ta Jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, da Majalisar Dattawan Kannywood wannan matsalar ta ɓatanci da Indabawa ya ke aikatawa, to amma babu wani hoɓɓasa da su ka yi a kai.

Ko a yau Talata sai da marubucin Facebook ɗin ya sake wallafa rubutun da ya fara jawo fitinar, wanda ya yi tun a bara, sannan ya maimaita maganar da ya faɗa a baya, ya ce, “Ina ƙara faɗa: mafi yawan ‘yan fim ba mutanen kirki ba ne kuma su na lalata tarbiyya. Duk wanda zai ƙyale mutanen kirki ya hidimta wa ‘yan fim shi ma ba mutumin kirki ba ne ko waye.”

Loading

Tags: Ahmad SarariAl-Amin Ciromaɓata sunaHamisu Iyan-TamaImam Aliyu IndabawaKannywoodKano State High CourtMOPPANshari'an.
Previous Post

Iyan-Tama ya gargaɗi masu damfara da sunan sa a Fezbuk

Next Post

Kotun Musulunci da Sufeto-Janar sun umarci ‘yan sandan Kano su binciki Ado Gwanja, Safara’u, Amude Booth da wasu ‘yan fim

Related Posts

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Next Post
Ado Isa Gwanja

Kotun Musulunci da Sufeto-Janar sun umarci 'yan sandan Kano su binciki Ado Gwanja, Safara'u, Amude Booth da wasu 'yan fim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!