• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Rikadawa: Ba mu kafa ƙungiyar 13×13 don mu karya wasu ba

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 21, 2022
in Labarai
1
Rabi'u Mohammed Rikadawa

Rabi'u Mohammed Rikadawa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN jarumin barkwanci kuma mai fitowa a matsayin uba a cikin finafinan Kannywood, Alhaji Rabi’u Mohammed Rikadawa, ya bayyana cewa ba su kafa ƙungiyar su ’13×13 Movement’ don karya wasu ba kamar yadda ake tunani.

 Jarumin, wanda a da aka fi sani da Dila, a yanzu kuma Baba Ɗan Audu, ya shaida wa mujallar Fim cewa: “Wannan ƙungiya ta 13×13 in ka ji wani na irin wannan magana bai san ta ba. 

“Na yi imani duk wanda ya ke cikin wannan ƙungiya ya san ta, kuma ya san me ake ciki, ba zai faɗi irin waccan magana ba, bai zagi kowa ba, na san kuma ba zai faɗa wa kowa baƙar magana ba. 

“Ƙungiya ce da ta ke ƙoƙarin gyara ɗabi’u da kuma  samun mutuncin mu da martabar mu a idanun jama’a su dawo. 

“Yanzu ta kai wasu na ganin mu a karkace mu ke. Wani abin ka yi da kyakkyawan zato, amma za ka ji ana zagi da wasu abu makamancin irin wannan.”

A kan dalilin kafa ƙungiyar, Rikadawa ya ce, “A cikin mu akwai masu yi iya ƙarfin su duniya ta sani, akwai masu yi duniya ba ta ma sani ba. Sai mu ka ga cewa akwai buƙatar jama’a su san abubuwan mu. Mu na zuwa gidan marayu, mu na zuwa IDPs, mu na zuwa gidan gyaran hali; akwai ɗaurarru waɗanda wani N10,000 ne ya sa aka ɗaure shi, wani N20,000, wani N30,000. Wani ya fi shekara takwas a haka a ɗaure, an kuma yanke tarar amma babu yadda zai yi. 

“In ka kula, irin waɗannan wuraren mu ke zuwa mu kwanto su, mu biya mu karɓo su, mu ɗauki jari mu ba su, mu ba su sutura. Don haka ba ɗan takara kawai mu ke magana ba, kuma billahil azimu duk wanda mu ka ziyarta, komai girman shi abu na farko da mu ke faɗa masa, ƙungiyar nan da ka ke ji da gani ba ta siyasa ba ce kawai. Mu dai abin da mu ka sa a gaba shi ne  mu kyautata rayuwar al’umma, na farko mu kalli mu kan mu cikin industiri ɗin, rayuwar mu ta kyautata, al’ummar da mu ke tare da su rayuwar su ta kyautata. Wannan shi ne babban burin mu.”

Ya ƙara da crwa ƙungiyar ta fara ne kamar wasa, lokacin da fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya yi tunani ya ga cewa ya kamata a yi irin wannan aikin.

Ya ce: “In ka kula, kusan kullum za ka ga ya ba wancan kuɗi, ya ba wancan mota, ya ba wancan mashin, ka ji ya gaji ya ba wancan gida. Sai ya ce to me ya sa sai shi kaɗai? Idan aka haɗu ai za a yi da yawa. 

“Da ya yi tunani sai ya fara tuntuɓar abokan sa na kusa da shi, irin su Aminu Ala, su ka zama su biyu, irin su El-Mu’az Birniwa, su ka zama su uku, irin su Kamilu Koko, su ka zama su huɗu. Haka, haka, kafin ka ce wani abu sai ya ga sun kai su sha uku daidai.

“Sai su ka ce, ‘Ai ko tunda haka ne tunda mun kai mu goma sha uku, kuma mun yarda za mu yi, to mu zo mu yi’. Su ka fara fita su na neman al’umma manyan ƙasa su zo su gaya masu abin da su ke ciki. 

“Da su ka fita ɗaya, biyu, sai su ka ga ta na da albarka. Sai su ka ce, ‘Bai kamata a ce mu mu kaɗai ba, mu jawo sauran. Mu sha uku ne, to kowa ya kawo mutum ɗaya’. 

“Ka ji yadda aka shigo ‘second batch’. To su sha uku sun kawo wasu mutum sha uku; 13 ga wata 13 ɗin, ka ga shi ne aka samu 13×13. Sai aka ga abin ya bunƙasa. Sai aka ce kowa ya kawo, yanzu mun haura mutum dubu in ma ba mu fi ba.”

A game da adawa da wata ƙungiyar makamanciyar ta da ‘yan fim su ka kafa, ɗan wasam ya ce: “Har yanzu ƙarya ne ka ji wani ɗan 13×13 ya zagi ɗan wata ƙungiya. Duk ma wani da ka ji ya zagi ɗan wata ƙungiya da sunan 13×13, ka je ka duba hotunan mu, za ka ga babu shi a ciki, ma’ana bai san abin da mu ke yi ba, shi ma sha’awar mu ya ke yi, sai ya ga cewa bari ya yi abin da za mu so shi, mu kuma cin mutunci ba zai sa mu so wani ba, duk wanda ya ke ciki za ka ga babu ruwan sa da kowa. Mu har dariya mu ke yi in mu ka ga wani na nema ya alaƙanta mu da wasu!

“Hatta ziyarar da mu ka riƙa yi, za ka ga mu na ziyartar ‘yan wasu jam’iyyun. Mu ba mu keɓe shehunnai ba, mu kai ziyara ga shehunnan da ba su a ɗariƙar mu. Ka ga ko da mun tsaya a ɗariƙa ɗaya ne, ai ba za mu yi haka ba.”

Rikadawa ya ci gaba da cewa, “Ƙungiyar da ake cewa an kafa 13×13 don a karya ta ne, mu na da kyakkyawar alaƙa da ita, domin duk ƙarya ne, babu wani wanda za ku haɗu da shi ka ce ba za ku gaisa ba. In ma wani ya zage ka ya na can gefen, in kun haɗu wallahi sai ka ga ya miƙo maka hannu, to kuma kai da ma ba ka ɗauka ya na yi ba, da ma kai zaman lafiya ka ɗauka ku na yi da shi. Da kun haɗu da shi ya yi maka sallama ka amsa ya wuce. 

“Ba ka taɓa ji ɗan nan da ɗan can sun yi bugi-in-buga ba. Kun taɓa ji har zuwa yanzu? Ka ga ai ana zaune ƙalau. 

“Saboda haka duk  in wani bai fahimta ba, ‘with time’ zai gane cewa ashe waccan tafiyar daban, ga abin ma da ake yi, ashe ma ba da mu su ke yi ba, mu ma mu je mu ci gaba da harkokin mu. Wannan shi ne kawai.

Ɗan wasan ya ƙarƙare da ba da shawara, inda ya ce: “Jan hankali guda ɗaya ne zan yi, ko ba ma a kan wannan tafiyar ba. A duk al’amari na rayuwa, in kai ka na  nan ka ji wani na daga can gefe, ku ku na nan ku na ku hira, sai ku ka ji wasu daga can gefe su na shewa su na dariya, to kada ku ɗauka da ku su ke yi, in ba su su ka jeho dutse su ka ce don uban ku da ku mu ke ba. 

“Kamar yadda sabgar nan ta daban ta haɗa ku, ku ma ku ɗauka wata sabga ce ta daban ta haɗa su.  Mutane su daina yamutsa al’amari, a ɗauki abu a zuciya a tunanin abu kaza kaza ne kawai, kawai shi kenan, kowa ya ɗauka haka ne, ba haka ba ne wallahi. 

“A riƙa yin abu da kyakkyawan zato, a riƙa duban abu da idon basira. Wannan shi ne rayuwa, ba wani abu ba.”

Rabi’u Rikadawa (Dila)

Mujallar Fim ta ruwaito cewa tun bayan da aka kafa ƙungiyar ’13×13 Movement’, wasu mutane daga cikin ‘yan Kannywood, musamman waɗanda ba su samu damar shiga ƙungiyar ba, sun riƙa ƙorafin cewa an kafa ƙungiyar ne don karya wata ƙungiyar.

Tun ba a bayyana wace ƙungiya ba ce har ta kai ga ana bayyanawa domin a lokaci babu wata ƙungiya sai ‘YBN Network Group’ ta babban furodusa Abdul Amart.

Sai dai duk surutan da ake yi ba za ka ji su sun fito daga bakin manyan ƙungiyar ba, sai dai mabiya. Hakan ya sa wata rana ciyaman na YBN reshen Jihar Kaduna, Abdullahi Abbas, da ciyaman na 13×13 reshen jihar, Lawandi Wassh, su ka haɗa mabiyan su su ka ɗauke su hoto tare domin nuna cewa duk ana tare. 

Daga baya, sai kowa ya gane cewa ƙungiyar 13×13 Movement ba don karya ƙungiyar ‘YBN Network Group’ aka kafa ta ba, kowace daga cikin su aikin ta daban.

A yanzu haka, biyu daga cikin fitattun ‘yan ‘YBN Network Group’, jarumai Lawan Ahmad da Garzali Miko, sun shiga 13×13 ɗin.

Loading

Tags: 13x13 MovementAbdul AmartAbdullahi AbbasAminu AlaBaba Ɗan AudubarkwanciDauda Kahutu RararaDilaEl-Mu'az Birniwa.Garzali MikoKamilu KokoƙungiyaLawan AhmedLawandi WasshRabi'u Mohammed Rikadawa.ubaYBN Network Group
Previous Post

Ba mu hana mutum miliyan 7 kammala rajistar mallakar katin zaɓe – INEC

Next Post

APC ta saka ‘yan Kannywood 5 cikin rundunar yaƙin neman zaɓen Tinubu

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
A sama: Rarara (a hagu) da Afakallah; a ƙasa, daga hagu: Moɗa, Nuhu da Jadda Garko

APC ta saka 'yan Kannywood 5 cikin rundunar yaƙin neman zaɓen Tinubu

Comments 1

  1. Pingback: Cewar Rikadawa: Ba mu kafa ƙungiyar 13×13 don mu karya wasu ba - LastNg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!