AN yi kira ga ‘yan fim da su yi amfani da irin darussan rayuwa da ke cikin wannan watan na Ramadana domin inganta rayuwa da kuma kyautata alaƙar su da juna.
Wata jaruma da ta jima a Kannywood, A’isha Tafida Gombe, ita ce ta bayyana hakan a lokacin tattaunawar ta da mujallar Fim.
A’isha ta ce: “Kamar yadda kowa ya sani, a yanzu harkar fim ta na buƙatar haɗin kai da kuma fahimtar juna a tsakanin masu gudanar da ita, don haka a matsayin mu na Musulmi da kuma yin imani da azumin watan Ramadan a matsayin jigo a cikin addinin Musulunci, ya na da kyau mu yi amfani da irin koyarwar da ta ke cikin sa domin inganta rayuwar mu da kuma sana’ar mu.”
Jarumar ta ci gaba da cewa, “Kamar yadda azumi ya zama wata makarantar koyon haƙuri da zama da yunwa da ƙishirwa, to ya kamata mu koyi haƙuri da junan mu da Allah ya haɗa mu. A cikin masana’anta ɗaya mu ke gudanar da neman kuɗi a tare, don haka mu zama mun fahimci junan mu da yadda za mu yi harkokin mu cikin mutunta juna.

“Duk wasu abubuwa da ake faɗa a kan mu, to mu ne mu ka bayar da ƙofa har ake yi mana hakan, domin idan mu ka zamo masu ganin mutuncin junan da ɓoye sirri, to wasu abubuwa da dama ba za a san da su ba. Domin ita rayuwa da ka sani kowa ya na ɓoye sirrin sa ne, shi ya sa ake ganin sa har ake sha’awar sa. Amma idan ya zama ba shi da sirri, to kowa a wulaƙance zai rinƙa kallon sa. Don haka mu sani ɓoye sirrin junan mu shi ne mutuncin mu a idon jama’a “
A game da mutanen da ke kallon ‘yan fim a matsayin waɗanda ba su da mutunci kuwa, A’isha Gombe ta ce, “Wannan abin sam ba haka ba ne. Laifin wasu ne ya ke shafar wasu. Domin akwai mutane da su su ka fi yawa ma a cikin masana’antar da su ke da mutunci kuma su ka samu tarbiyya a gidan su, don haka ba duk aka taru aka zama ɗaya ba. Don ko ni ina alfahari da tarbiyyar da na samu a gidan mu, wadda ita ce ta sa na samu rayuwa mai ingancin da na ke alfahari da ita.
“Don haka mu ‘yan fim mu na da mutuncin mu. Ko da an ji wasu abubuwa da aka ce ana yi, to daga wasu ne, ba duk ‘yan fim ɗin ba ne su ke yin hakan.”
A’isha Tafida Gombe dai tsohuwar jaruma ce da ta shafe sama da shekara goma a harkar fim. Ta yi finafinai masu yawa da marigayi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro) da su Ali Nuhu, sa’annan a can baya ta fita a cikin ‘Kwana Casa’in’.
A yanzu ta fi fitowa a waƙoƙi da kuma tallace-tallace na kamfanoni da waƙoƙin siyasa.
