• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Kano ta soke lasisin duk masu gudanar da harkar fim

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 28, 2023
in Labarai
0
Alhaji Abba El-Mustapha

Alhaji Abba El-Mustapha

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta soke dukkan wata takarda ta ba da izinin gudanar da duk wani aiki a masana’antar Kannywood a jihar.

Dokar ta shafi jarumai furodusoshi, daraktoci, masu ɗaukar hoton fim, masu kwalliya, kamfanonin shirya fim da duk wani aikin shirin fim. 

Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Musatapa, shi ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya rattaba wa hannu a yau Juma’a, 28 ga Yuli, 2023 

A lokacin da yake yi wa mujallar Fim ƙarin bayani dangane da sanarwar, El-Mustapha ya ce: “Wannan mataki ya zama dole a ɗauke shi domin kawo gyara da kuma tsaftace sana’ar fim saboda wani hali da ta shiga. Don haka an dakatar da lasisin duk wani ɗan fim har zuwa nan gaba da za a samar da wani tsari na ba da lasisin cikin yanayi mai kyau.

“Don haka duk wani lasisi da ya ke hannun mutane ko wani katin shaida daga yanzu ya daina aiki.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an daɗe ana ƙorafi kan yadda ake bayar da lasisin shiga harkar fim, musamman yin rajista ga jarumai da kuma katin shaida wanda wasu su ka mayar da shi wata harkar kasuwancin da su ke samun ƙazamar riba a wajen duk wata baƙuwar mace da ta shigo Kano da sunan za ta yi fim.

Mutanen da su ke aikata hakan da sunan cewa su furodusoshi ne ko daraktoci su kan tatsi mata kuɗi da sunan za su yi masu rajista da hukumar tace finafinai ta ƙarƙashin kamfanonin su.

Akwai wani furodusa da wata yarinya ta daga Nijar a shekarar da ta gabata inda ya karɓi kuɗi N100,000 a wajen ta da sunan zai yi mata rajistar da kuma katin shaida na Hukumar Tace Finafinai.

Haka ma akwai wani darakta da wata yarinya da ta zo daga Taraba ta kai ƙarar sa ga hukumar a kan ya karɓi kuɗin ta N80,000 da sunan zai samo mata katin shaida na hukumar a cikin mako guda, amma sai aka shafe tsawon watanni ba tare da ya samo mata ɗin ba. 

Sannan wasu su kan yi amfani da wannan damar ta yadda karuwai su ke fitowa daga cikin Sabon Gari su yi rajista da hukumar ta yadda duk inda su ka je aka kama su sai su ce su ‘yan fim ne.

El-Mustapha bai faɗi tsawon lokacin da wannan soke lasisin zai kai ba.

Loading

Previous Post

Matan Kannywood sun yi gargaɗi kan ‘yan damfara masu amfani da sunan su a soshiyal midiya

Next Post

Kiran mawaƙi Auta Waziri ga abokan sana’ar sa: kada mu dogara da waƙa ita kaɗai

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Abdullahi Abubakar (Auta Waziri)

Kiran mawaƙi Auta Waziri ga abokan sana'ar sa: kada mu dogara da waƙa ita kaɗai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!