BABBAN Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana jin daɗi saboda sake buɗe makarantar koyon sana’ar shirya fim da ke garin Tiga da gwamnan jihar ya yi kwanan nan.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya ambato sakataren, kuma ya ce El-Mustapha ya taya murna ga sabon daraktan makarantar, Dakta Maigari Indabawa.
El-Mustapha ya ce, “Mai girma gwamna ya yi abin da ya dace, duba da yadda sana’ar finafinai ke buƙatar sauyi ta fuskar ilimi, wanda hakan zai bunƙasa tattalin arzikin Kano tare da kawo kuɗin shiga.”
Ya ƙara da cewa, “Da yawa daga cikin ‘yan masana’antar na buƙatar samun ƙaro horo, domin a nuna masu sababbin dabaru ta yadda sana’ar za ta tafi da zamani. Haka kuma su kan su ‘yan masana’antar za su yi gogayya da takwarorin su na ƙasashen waje.”
Shugaban hukumar ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da yi wa sabon shugaban makarantar fatan alheri da addu’ar Allah ya sa ya fara a sa’a, ya kuma gama lafiya.
Haka kuma babban sakataren ya yi wa sauran waɗanda aka naɗa muƙamai daban-daban fatan alheri da addu’ar samun nasara a dukkan ayyukan su.