MAHAIFIYAR tsohuwar jaruma a Kannywood, Hadiza Maina, wato Hajiya Habiba Yusuf, ta rasu.
Marigayiyar, mai kimanin shekara 60 a duniya, ta rasu a jiya Talata, 12 ga Satumba, 2023 da misalin ƙarfe 5:30 na yamma a Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, sakamakon jinya da ta yi ta tsawon wata ɗaya.
An yi mata sallah da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Laraba, 13 ga Satumba, a gidan ta da ke lamba, 3 layin SCOA, kusa da Kaduna Motors, a unguwar Shanu, Kaduna.
Ta bar ‘ya’ya tara, maza shida, mata uku. Hadiza Maina ce ta uku a cikin su.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ‘yan fim da su ka halarci jana’iza da kuma waɗanda su ka je ta’aziyya ya zuwa yanzu sun haɗa da Abdullahi Maikano, Al-Amin Ciroma, Murtala Aniya, Sabi’u Gidaje, Alhaji Yusuf Gidaje, A’isha B. Umar, da A’isha Adamu.
Allah ya jiƙan Hajiya Habiba, amin.
