A JIYA Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023 aka yi taron walima na saukar karatun Alƙur’ani na ‘yar Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, wato Aisha Abba El-Mustapha (Lateefa).
Taron ya gudana da yamma a gidan El-Mustapha da ke Titin Malam Aminu Kano, kusa da Ƙofar Gadon Ƙaya, a birnin Kano.
A wajen taron, wanda ‘yan’uwa da abokan arziki da dama su ka halarta, an yi karatun Alƙur’ani tare da addu’o’i, sannan kuma aka raba kyaututtuka ga yara. Ita ma amaryar saukar, wato Aisha, ta gabatar da karatu.

Da ya ke jawabi dangane da taron, El-Mustapha ya ce ya shirya wannan taron ne domin ya nuna godiyar sa ga Allah da ya ba shi arzikin haihuwar ‘ya mai basira da ƙwazo, domin kuwa ta na shekaru 14 da haihuwa a duniya ta yi saukar Alƙur’ani, kuma sauka ba ta zuƙu ba, sauka ce ta hadda.
Ya ce: “Ina godiya ga Allah da wannan arzikin da Allah ya yi mani, kuma zan kasance mai alfahari da wannan baiwa har ƙarshen rayuwa ta.
“Allah mun gode maka, kuma muna ƙara godiya a gare ka da wannan baiwa.
“Kuma ina fatan duk waɗanda su ka zo wannan waje da ma waɗanda ba su samu damar zuwa ba Allah ya haɗa mu a ladar.”
‘Yan fim da dama sun halarci wajen, daga cikin su akwai Mustapha Ahmed (Alhaji Sheshe) da Bashir Abubakar Maishadda.




Comments 1