ALLAH ya yi wa shahararren malamin addinin nan da ke Kano, Sheikh Yusuf Ali, rasuwa.
Shehin, wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya, ya rasu a daren jiya Lahadi a Kano ya na da shekara 73 a duniya.
Babbar ‘yar sa, Hajiya Bilkisu Yusuf, wadda malama ce a Jami’ar Alqalam da ke Katsina, ta bada sanarwar rasuwar a Facebook.
An haifi Sheikh Yusuf a garin Gaya, Jihar Kano, a cikin 1950.
Ya fara aikin shari’a a matsayin magatakarda a Kotun Shari’a ta Kano a cikin 1974, kuma ya riƙa samun ƙarin girma har ya kai Babban Kilak, ya zama Mataimakin Magatakarda, ya zama Alƙalin Babbar Kotun Shari’a, sannan ya zama Darakta a Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Kano.
Sheikh Yusuf Ali ya yi ritaya daga aikin gwamnati a cikin 2009, inda daga nan ya ci gaba da yin wa’azi da koyarwa a gidan sa da ke Tudun Maliki kusa da Gidan Zu.
Za a yi jana’izar sa a gidan nasa a yau Litinin da ƙarfe 1:30 na rana.