HARKAR fim da ake yin ta yanzu a Kannywood ta yi hannun riga da koyarwar addinin Musulunci, a cewar mawaƙin siyasa mazaunin Kaduna, Alhaji Ibrahim Sale Yala.
Mawaƙin ya na magana ne kan hayaniyar da ta baibaye masana’antar a soshiyal midiya sakamakon kalamin da jarumi Abdalla Amdaz ya yi a gaban shugabannin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a cikin wannan makon, kalamin da wasu ‘yan fim ke ganin tozarci ne ga masana’antar.
Yala ya ce mutane sun ƙi karɓar gaskiya ne kan abin da Amdaz ya faɗa, kuma shi ɗin ma ya sha yin maganganu irin waɗannan a baya amma aka yi biris da shi.
A rubutun da ya yi a soshiyal midiya a yau, mawaƙin, wanda ya taɓa yin fice da wata waƙar Janar Muhammadu Buhari a shekarun baya, ya ce: “Mafi yawan musibu su na faruwa ne daga kangare wa ɗaukar wa’azi ko wasun ku su janyo muku. Ni Ibrahim Yala na sha yin maganganu irin na Amdaz ko ma waɗanda su ka fi nashi zafi domin a samu gyara a wannan masana’anta da Allah ya ƙaddara sai an gan mu a cikin ta.
“Wallahi thunma tallahi wannan harkar ta yi hannun riga da Allah tun tuni, sai dai idan ba za mu faɗi gaskiya ba saboda son rai ko jahilci na rashin sanin halal da haram.”
A nadamar da ya yi ta kasancewar sa ɗan Kannywood, mawaƙin ya ce ba ya sha’awar wani nasa ya shiga harkar fim ta hanyar sa ko kaɗan.
“Wallahi ni ba ma ɗan da na haifa ba ko wanda ban da alaƙa da shi – in dai sanadi na zai shiga fim – ba zan bari ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Masana’antar da babu mai ganin girman wani saboda yawancin mu mun zubar da mutuncin junan mu. Babu albarka a abin da mu ke kira sana’a saboda mun kauce wa duk wani tsari na addini. Babu mai sawa ko hanawa a cikin masana’antar.”
Ga masu ganin laifin Amdaz kuwa, Yala ya ce: “Kun san gaskiya sai dai ku bi son rai, amma duk abin da aka faɗa ana aikatawa babu sharri ko son rai a ciki.”
Ya ce a kullum ya na nadamar zaman sa a Kannywood. “Wallahi ban taɓa tsintar kai na a harkar da kullum ta ke fita a rai na ba irin wannan harkar tamu,” inji shi.
Dangane da yadda wasu fitattun matan Kannywood su ke kece raini da dukiya kuwa, sai Yala ya ce: “Na taɓa magana da wani a kan yadda matan masana’antar da su ka yi suna su ke yi na rashin kamun kai da gadara gurin saɓa wa tsarin addini, sai ya ce, ‘Waɗannan yaran kusan su su ke riƙe da masana’antar domin ɗai ɗai wanda ba su bai wa kuɗi.’ Shi ya sa za ka ga yarinya ta yi ‘posting’ a bakin hotel bayan kwashe kwanaki ta na holewar ta, har ma ka ga ta rubuta, ‘Alhamdu lillah,’ sai ka ga kowa na tura mata ‘WOW, kin yi kyau!’ ko hoton alamar zuciya, ko wuta balbal.'”
Yala ya ƙara da cewa,”Ni da ku mun san sana’ar ta ba fim ba ne.
“Sannan haka wasu mazan cikin mu sun zama abokan hulɗar ‘yan siyasa waɗanda ba su da juriyar zama babu kuɗi, su miƙa kan su ko su zama kawalai ta kowacce irin siga.”
Mawaƙin ya ce a kan waɗannan zarge-zarge shi ganau ne ba jiyau ba, domin wani abin ma ya shafe shi kai-tsaye.
“Idan na ce zan ci gaba da rubuta abubuwan da na sani game da wannan masana’antar, gaskiya za a sha mamaki domin wasu abubuwan ma sun shafe ni kai-tsaye wallahi,” inji shi.
A ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya “shiryar da mu hanya madaidaiciya, amin.”