A DALILIN Ali Nuhu:-
- Tsofaffin ‘yan Kannywood da sababbi sun haɗu waje ɗaya rana ɗaya sun ƙulla zumunci da juna.
- Manyan dattijai na Kannywood da yara sun haɗu don sada zumunci.
- Fuskokin da aka daɗe ba a gani ba sun bayyana an gan su.
- Waɗanda ke takun saƙa da juna sun haɗu wajen ɗaya har sun gaisa.
- Iyalai da su ka rabu a matsayin ma’aurata sun haɗu sun gaisa da juna.
- Mutanen gari da ‘yan Kannywood sun haɗu sun gaisa.
- An ɗabbaƙa sabon tsarin taro mai suna Kannywood Day da za a riƙa gudanarwa duk ranar 5 ga Fabrairu na kowace shekara domin taimakekeniya ga juna.
- An samu taimakekeniya da gudunmawa ga juna fili da ɓoye.
- Mutanen gari sun shaida haɗin kai da kara tsakanin ‘yan Kannywood.
- Arziki ya yaɗu ta inda kasuwanci ya ɗan ƙara motsawa a kasuwar arewacin Nijeriya.
- An samu ƙarin matsawa cikin gwamnati sama da ta ƙasa.
- An samu damar shiga tsarin ƙasashen duniya don aiwatar da tsarin tafi da shirin finafinai daidai da zamani.
- Gwamnati ta nuna wa duniya cewa ɗan fim ba wai fim kaɗai ne abin da ya ke iyawa ba, kai har ma da mu’amalar tafi da gwamnati.
Tabbas, waɗanda su ka shirya wannan taro sun yi tunani mai zurfi. Ita kuma gwamnati da ta ba Ali Nuhu wannan muƙami ta taimaki masana’antar Kannywood da Nollywood matuƙa da gaske wajen girmama ɗan cikin su da wannan muƙami.
* Muddassir Ƙassim fitaccen mawaƙi ne a Kannywood
![]()







