ZULYADAINI, babban ɗan jarumi a Kannywood, Alhaji Isa Bello Ja, wanda ake yi wa laƙabi da Dattijon Arziki, zai yi mata ta biyu a ranar Asabar mai zuwa.
Za a ɗaura auren Zulyadaini da sahibar sa Hindatu Abubakar Abdullahi da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gidan sarkin ƙauyen Kabagiwa da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.
Kamar yadda katin gayyatar ya nuna, za a haɗu da ƙarfe 11:00 na safe a Gidan Mai na Gade-Gade da ke kusa da gidan Rediyon Premier, a Hotoro, Kano.
Allah ya kai mu ranar da rai da lafiya.