ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, tare da haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta jihar, sun ƙara wa’adin rajistar ‘yan fim.
Shugaban ƙungiyar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce, “Biyo bayan koke-koken ‘yan fim na a ƙara wa’adin rajistar, yanzu haka ƙungiyar ta ƙara wa’adin zuwa 28 ga wannan wata, tare da umartar dukkanin waɗanda ba su yi rajistar ba da su yi gabanin cikar wa’adin.”
Haka kuma, shugaban ya ce, “Wa’adin na 28 ga Fabrairu na zaman wa’adi na ƙarshe da ƙungiyar za ta bai wa mambobin Kannywood.
“Kuma ƙungiyar ta MOPPAN da Hukumar Tace Finafinai za su ɗauki matakin ba-sani-ba-sabo ga dukkanin waɗanda ba su yi rajistar ba har idan wa’adin ya cika.
“Don haka kowane jarumi ya tabbatar ya je ofishin ƙungiyar MOPPAN da ke kan titin zuwa Jami’ar Bayero, kusa da ofishin darakta Ismail Khalil Ja’en, domin yin rajistar.”
Da farko a yau, Talata, 20 ga Fabrairu, ne ranar ƙarshe da za a rufe yin rijistar, amma an ƙara kwanaki takwas, wanda ya kama ranar Laraba, 28 ga Fabrairu kenan za a rufe rajistar.
![]()







