MAWAƘI a Kannywood, Malam Sanusi Ɗahiru Pambeguwa, ya na gayyatar ‘yan’uwa da abokan arziki zuwa ɗaurin auren ‘yar sa, Fatima.
Za a ɗaura auren Fatima Sanusi Pambeguwa da sahibin ta Yusuf Sani a ranar Asabar mai zuwa da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gidan marigayi Alhaji Ɗahiru Dillalin Masara, Pambeguwa, Jihar Kaduna.
Malam Sanusi ya ce ya na gayyatar kowa da kowa, kuma wanda bai samu damar halarta ba ya yi addu’a, ya san halin da ake ciki.
Allah ya kai mu ranar.
![]()







