ALHAJI Habibu Barde Muhammad shi ne sabon Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) da ya kama mulki bayan saukar da tsohon shugaban, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya yi a ƙarshen watan Janairu na bana. Kafin haka, shi ne Mataimakin Shugaba na Arewa ta Tsakiya na ƙungiyar.
Mujallar Fim ta zanta da shi domin jin wanene da kuma irin gudunmawar da ya bayar a harkar fim.
FIM: Kafin kasancewar ka Shugaban MOPPAN za mu so ka ɗan yi wa masu karatu bayani game da gudunmawar da ka bayar ga harkar fim da abin da ka sa a gaba a yayin gudanar da jagorancin ka na tsawon shekara guda da za ka yi.
HABIBU BARDE MUHAMMAD: To, ni dai na fara harkar ƙungiyoyin diramar Hausa a Bauchi tun 1979 bayan sakandare da BACAS ƙarƙashin ‘Bauchi State Theatre Group’ na zamanin.
Na fara aiki a matsayin Assistant Producer a Bauchi Radio Corporation a 1980.
Na tafi Columbia College, Hollywood, ƙaro ilimi, a inda na yi diploma a Television/Radio Production a 1983. Na yi B. MA. degree na gama a 1985 a Television/Radio Productions.
Na dawo gida na yi NYSC a NTA Television College, na gama a Disamba 1986.
Na koma BRC Bauchi aiki a Janairu 1987 a matsayin Producer 2.
Daga buɗe Bauchi State Television Authority an maida ni wajen a matsayin Producer 1 a 1989.
Janairu 1990, Hukumar MAMSER, wato NOA yanzu, ta ɗauke ni aiki a hedikwatar ta a Abuja a matsayin Senior Information Officer mai shiryawa da gabatar da shirye-shiryen su na wayar da kan jama’a a Radio Nigeria Kaduna.
Na bar NOA na koma main Federal Service a matsayin Assistant Chief Administrative Officer a Presidency Council Secretariat a Nuwamba 1998.
Na yi aikin administration on posting to ma’aikatun Gwamnatin Tarayya kamar Culture and Tourism a matsayin P. A. to the Permanent Secretary, Ministry of Agriculture, Defence Ministry under joint services Department Special Services Section na tsawon shekara biyar, daga 2004 zuwa 2009.
An maida ni Mataimakin Darakta a Federal Ministry of Youth Development bayan na kammala Masters degree a ABU Zaria a fannin International Affairs and Diplomacy.
Bayan shekaru aka maida ni Federal Ministry of Interior, Business and Citizenship Department a matsayin Mataimakin Darakta. 2014 aka maida ni Federal Ministry of Transportation, Maritime Services Department, a inda na yi ritaya a Directorate Cadre level a watan Maris 2019 at the age 59, having served the 35 years in service of my country.
Kuma a duk tsawon wannan lokacin kuma ina harkar talbijin da rediyo tare da abokai; na yi a Kannywood, being my main professional field.
Yanzu bayan ina gudanar da ayyukan productions nawa na rediyo da talbijin ƙarƙashin kamfani na Hashwannar Nigeria Ltd a nan Abuja da Kano.
Shi ne yanzu BOT ta MOPPAN ta naɗa ni a matsayin sabon Shugaban MOPPAN na ƙasa zuwa lokacin da za a yi zaɓen sababbin shugabannin ƙungiyar na ƙasa a shekara mai zuwa in-sha Allah.
FIM: Da yake shekara ɗaya ya rage maka za ka yi, ko me ka shirya za ka gudanar a cikin shekarar?
HABIBU BARDE MUHAMMAD: To, da man da ni aka gudanar da shugabancin na shekara biyu, ina matsayin Mataimaki na Arewa ta Tsakiya, don haka duk da ni ake gudanar da komai. Kuma alhamdu lillahi Dakta Ahmad Muhammad Sarari ya ɗaukaka darajar MOPPAN ya kai ta ƙololuwa, don haka duk abin da za mu yi sauran abin da ya rage ne, saboda shi jajirtaccen shugaba ne. Abin da za mu yi shi ne za mu tsara zaɓe. Wannan ya sa ma a yanzu na zo Kano. Mun yi zama na Majalisar Ƙoli ta MOPPAN ɗin wanda mu ka tattauna a kan yadda za mu gudanar da ayyukan da za mu yi cikin shekara guda ɗin da aka ba mu.
Kuma da man na faɗa maka za mu ƙarasa shekarar da shi Dakta Ahmad Muhammad Sarari ne, to amma kowanne shugaba akwai wani tsari da yake da shi wajen gudanar da nasa shugabancin, don haka akwai wasu ƙudirori da za mu gudanar wajen namu shugabancin. Don haka mun zaɓo wasu jigajigan mutane daga kowanne ɓangare na jihohin da mu ke da su domin tsara yadda za a samar da yanayin da za a gudanar da zaɓe da kuma yadda za mu ɗaukaka MOPPAN ɗin yadda shugabanni da za su zo su same ta a kan saiti.

Sannan mun samar da kwamitin gyara tarbiyyar ‘yan wasa duk da sauran kwamitocin. Za mu yi aiki na wata uku, mu zagaya ƙasar nan domin gudanar da ayyukan mu da neman kuɗin da za mu gudanar da zaɓen da za mu yi da kuma kawo gyara a cikin masana’antar kuma alhamdu lillahi ina da ƙarfin gwiwa a game da ‘yan kwamitin da za mu yi aiki da su masu kishin harkar ne, masu son ganin gyaran ta ne. Kuma ni a matsayi na na shugaba ina son ne kawai na gudanar da zaɓe, don ba ni da niyyar na tsaya takara saboda ina da wasu ayyuka na da na ke buƙatar na gudanar, kuma ga shekaru na a yanzu sun kai na tsaya na huta na samu isasshen lokaci. Don haka na ce da su ba zan nemi wata takara nan gaba ba; zaɓe kawai zan tsara mu ga mun samar da tsari mai inganci da zai saita masana’antar.
Kuma in Allah ya yarda ba zan zo na nema ba. Duk yadda aikin ya yi mini daɗi a haka zan bar shi don na je na samu hutu tare da gudanar da ayyukan da su ke gaba na.
FIM: Wanne buri ka ke da shi a tsawon shugabancin da za ka yi na shekara guda?
HABIBU BARDE MUHAMMAD: To, gaskiya buri na na samar da tsarin zaɓe mai kyau yadda za a samu shugabancin da za a ji daɗin sa, wanda hakan zai sa a rinƙa tunawa da ni a tarihin masana’antar. Kuma da tabbacin zan yi hakan da fatan goyon samun goyon baya daga waɗanda za mu yi aiki tare don ganin an kai ga cimma wannan buri da na ke da shi.
FIM: To madalla, mun gode.
HABIBU BARDE MUHAMMAD: Ni ma na gode.