IRIN abin nan da ake kira “mun zo garin ku mun fi ku rawa” ya faru ga ɗimbin ‘yan fim da mawaƙa jiya a Kaduna a wajen bikin ganin sabuwar shekara.
Gwamnatin Jihar Kaduna ce ta shirya bikin, amma da aka zo sai ta yi watsi da ‘yan fim da mawaƙa na jihar, ta rungumi ‘yan Kudu.
A karon farko dai, gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya bikin na shigowar sabuwar shekara ta 2020, wanda ta yi wa laƙabi da ‘Countdown’.
Bikin gagarumi ne, wanda ba a taɓa yin sa a Kaduna ba ko kuma a faɗin Arewa gaba ɗaya in ban da Abuja.
Tun da aka shiga watan Disamba 2019 gwamnatin jihar ta fara tallar bikin a shafukan ta na soshiyal midiya.
Gwamnatin ba ta manta da ‘yan fim da ke jihar ba wajen gayyata, domin kuwa ta gayyace su, kuma sun amsa kira.
Tun ana saura kwana biyu a gudanar da bikin aka kira wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a na masana’antar fim aka ba su tikitin shiga wurin domin su raba wa mutanen su kyauta.
A ranar Talata, 31 ga Disamba, 2019 aka gudanar da bikin.

An buɗe wurin taron da misalin ƙarfe 6:30 na yamma. Wurin taron mai suna Centenary Park da ke daura da gidan gwamnan jihar a Kaduna.
Wurin ya cika maƙil da jama’a.
A baya sunan wurin Galaxy Amusement Park, a yanzu kuma an raɗa masa suna da Centenary Park, wanda ake cikin ƙayata shi don jin daɗin jama’a.
‘Yan fim da sauran jama’ar gari sun fara hallara a filin taron tun da aka buɗe ƙofar shiga.
Nan kowa ya ci gaba da shaƙatawa, domin an tanadi wurare na musamman domin ɗaukar hoto da kuma kuma wurin wasan yara.
Jami’an gwamnatin Jihar Kaduna sun iso wurin da misalin ƙarfe 9:00 dare. Daga cikin su akwai Mataimakiyar Gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe, da shugaban ma’aikatan jihar, Muhammad Sani Dattijo, da Honarabul Ali Chakis, da mai ba gwamna shawara kan matasa da shaƙatawa, Hajiya Halima Idris, da sauran su.
An sa kuɗin tikitin shiga na manya N1,500, na yara kuma N500.
‘Yan fim da mawaƙa da dama sun halarci bikin.
Amma duk da amsa gayyatar da su ka yi, ba a ba su wani muhimmanci ba a wurin, domin ana iya cewa su ma dai kawai sun je kallo ne kamar kowa, don ba a ba su wata dama ba ko kaɗan.
Akwai mawaƙa ‘yan wasan barkwanci da su ka shirya yin wasa a wurin, amma abin ya ci tura. DJ Emzor ya yi ta saka waƙoƙi, amma babu ta Hausa ko ɗaya a cikin su, sai na ‘yan Kudu, duk da cewa shi ma DJ Emzor ɗin ya na daga cikin ‘yan masana’antar Kannywood.
Wasu sun ce ta yiwu umarni ne daga wurin waɗanda su ka shirya bikin.
Wani mawaƙi ya labarta wa mujallar Fim cewa Hajiya Halima Idris ta so a ba su dama don su yi wasa a wurin, amma sauran jagororin su ka ƙi yarda, su ka ce sai dai a ɗauko mawaƙan Kudu.
Duk da hakan Hajiya Halima ta ce a haɗa su gaba ɗaya, amma su ka ce ba su yarda ba. Dole sai haƙura ta yi.

Amma kuma ana saura mintI 30 a fara ƙirgen daƙiƙun da su ka rage a shiga shekarar 2020, wanda da ma shi ya tara mutane a wurin, sai aka ga fitaccen mawaƙin Kudu, M.I. Abaga, ya ɓulla kan dandamali, inda ya fara baje kolin sa har lokaci ya yi aka fara ƙirgen.
Wannan ya nuna ƙarara cewa ba a ba ‘yan fim da mawaƙan Kaduna muhimmanci a wurin ba.
Sai dai kuma wani abin burgewa, ‘yan fim ɗin da mawaƙan ba su damu ba, ko a ce ba su nuna ba. Sun ci-gaba da hidindimun su kamar yadda kowa ya ke yi a wurin.

‘Yan fim da mawaƙa da su ka halarci bikin sun haɗa da Fatima Ibrahim Lamaj, Sagir Baban Kausar, Musa Mohammed Abdullahi, Ibrahim Al-Imash, Nura MC, Abbas Sadiq, Ahmad Yariman Tiga, Isama’il Koli, Beatrice Williams Auta, Sabi’u Gidaje, Hafsat Jos, Yusuf Gidaje, Garba Shehu PS, Wassh Waziri Hong, Lawandi Wassh, A.A. Rasheed Kabala, Buhari Ɗansoja, Abubakar Hunter, Ali Artwork, Hudu Mazaje, Abubakar Shinko, Ɗayyab Maiɗa’a, Jamilu Ɗanmasukuɗi, M. Suraj, da sauran su.