A DAIDAI lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ta fara shirye-shiryen zaɓen ƙananan hukumomi, fitaccen jarumi Sani Musa Danja ya fito takarar Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar.
Duk da kasancewar sa jarumi ne da ya yi fice a fagen siyasa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya, fitowar tasa takara ta zo wa mutane a bazata.
Ba a taɓa jin Danja a fagen neman wani muƙami ba, duk kuwa da irin rawar da ya taka a lokacin gwamnatin ‘Yar’Adua da ta Jonathan.
A wancan lokacin, ya ja zaren sa yadda yake so har ana ganin in da yana da buƙatar neman matsayi da ya nema a gwamnatin Jonathan.
Wannan ta sa wasu su ke ganin ko dai a yanzu Danja ya fito ne domin kawai ya tayar da ƙura kuma ya gwada tasirin sa a siyasa.
Mujallar Fim ta ga yadda hotunan jarumin na takarar shugabancin ƙaramar hukumar sun fara yawo a cikin garin Kano da soshiyal midiya.