FITACCIYAR ‘yar wasan talabijin ɗin nan na ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa24, Hajiya Zahra’u Sani, wadda aka fi sani da Adama matar Kamaye, ta bayyana irin fitinar da ta ke yi wa mijin ta a cikin shirin da cewa ba halin ta ba ne na zahiri. Ta ce kawai dai labarin ne ya zo da haka, kuma a duk lokacin da jarumi ya ke son ya isar da saƙo ga al’umma, to sai ya yi abin da rol ɗin da ya hau ya zo da shi.
Zahra’u ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da mujallar Fim dangane da rol ɗin nata.
Tun da farko sai da jarumar ta bayyana mana asalin ta da kuma yadda aka yi ta shigo harkar fim.
Ta ce: “To ni dai Zahra’u Sani, wadda aka fi sani da Adama matar Kamaye a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, asali na ‘yar Gombe ce, a can aka haife ni, na tashi a can, na yi makaranta, sai kuma daga baya na dawo nan Kano na ci gaba da zama a wajen ‘yan’uwa na”.
Dangane da yadda ta samu shiga harkar fim kuwa, cewa ta yi, “Ina ganin kusan shekaru goma kenan da shigowa ta harkar fim, kuma na shigo ne ta sanadiyyar aminiya ta, wato Hajiya Zulai Bebeji, wadda ita ce na same ta na nuna mata sha’awa ta ta yin fim.
“Kuma a lokacin mu ka tafi; da man za ta je lokeshin, don haka ta tafi da ni, kuma mu na zuwa aka saka ni a fim wanda kuma shi ne fim ɗi na na farko, sunan sa ‘Kazar Tsafi’.
“Kuma tun daga lokacin na ci gaba da yin fim har zuwa yanzu.”
To yaya aka yi ta samu kan ta a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’?
Zahra’u ta ce, “To gaskiya zan iya cewa al’amari ne daga Allah, domin an kira mutane ne za a tantance su, ni ma sai na je don na gwada sa’a ta, kuma Allah ya sa na dace aka ɗauke ni a matsayin Adama.”
Da ya ke da fim ɗin kasuwa ta fara, mun tambaye ta bambancin fim ɗin kasuwa da fim mai dogon zango irin na talabijin.
Amsa: “To gaskiya ni a gani na tazara ce kamar tsakanin sama da ƙasa, domin kuwa shi wannan duniya ce ga baki ɗaya ta ke kallon ki, shi kuma na kasuwa sai wanda ya saya ya kai gidan sa, don haka fim ɗin ‘Daɗin Kowa’ ya fi karɓuwa a wajen mutane, domin na yi fim tsawon lokaci, amma ka ga mutane ba su san ni ba sai a ‘Daɗin Kowa’, don haka ‘Daɗin Kowa’ ne ya ɗaga ni duniya ta san ni.
“A baya ana ganin mu jifa-jifa a ce an san mu, amma kuma da mu ka shiga ‘Daɗin Kowa’ sai kowa ya san mu.
“Yanzu za ka shiga taro sai ka na ɓuya, saboda idan mun shiga gari mu ka haɗu da yara, mu na fuskantar matsaloli, saboda ƙauna sai mutum ya ce wai sai ya taɓa jikin ka. To ka ga idan wannan ya taɓa wancan ya ce zai taɓa, sai su yaga maka kaya, ko kuma su cire maka gyale.
“To wannan shi ya sa mu ke gudun yara wani lokacin, ko mu saka niƙab mu rufe fuskar mu in za mu fita.”
Zahra’u ta bayyana cewa irin gajiyar da ta ci da shirin ‘Daɗin Kowa’ “abin ba zai lissafu ba.”
A cewar ta, “Har zuwa yanzu mu na cin gajiyar ne kuma za mu ci gaba da ci nan gaba. Don haka a wannan ɓangaren babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah.”
Daga ƙarshe, ta yi kira ga jama’a da su fahimci cewar yadda ta ke rayuwa a cikin ‘Daɗin Kowa’ ba haka rayuwar ta ta zahiri ta ke ba. “Domin wani lokacin na kan samu kai na wasu su tsare ni su rinƙa yi mini tambayar me ya sa na ke yi wa Kamaye abu kaza. To haka rol ɗin ya zo, don haka ba hali na ba ne.”