• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda na rikiɗa daga mawaƙi zuwa jarumi a ‘Kwana Casa’in’ – Auwal Ishaq

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 5, 2020
in Taurari
0
Auwal Ishaq, mai taka rol ɗin Yawale Ɗankurma a cikin 'Kwana Casa'in'

Auwal Ishaq, mai taka rol ɗin Yawale Ɗankurma a cikin 'Kwana Casa'in'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
A DA an fi sanin Auwal Ishaq a fagen waƙa inda ya shahara matuƙa. Yanzu kuwa ya rikiɗe ya zama fitaccen jarumi a shirin gidan talbijin na Arewa24 ɗin nan mai suna ‘Kwana Casa’in’, inda ya ke taka rol ɗin Yawale Ɗankurma.
 
Abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne ba a yanzu ba ne Auwal ya fara zama ɗan wasa. Ya daɗe a haka, tun ya na waƙa. Yanzu da tauraruwar sa ta ke haskawa ne ake masa kallon sabon jini a fagen wasa.
 
Domin jin yadda ya samu kan sa a cikin ‘Kwana Casa’in’ da kuma wasu abubuwan, mujallar Fim ta tattauna da shi inda ya fara da ba mu amsa kan yadda aka yi ya rikiɗa zuwa fitaccen jarumi.
 
Auwal ya ce: “To ka san ita duniya juyi-juyi ce. A baya ina matsayin mawaƙi daga 1999 har zuwa 2019, kuma a yanzu dai zan iya cewa na rikiɗe na zama jarumi, wanda na ke taka rol a cikin ‘Kwana Casa’in’ a matsayin Yawale Ɗankurma.”
 
Shin ya jingine waƙa kenan?
 
“To zan iya cewa Hausawa su na cewa kowa ya bar gida…, don haka ina nan a fagen waƙa, don sai ma abin da ya ƙaru. Ko da na zama Yawale a yanzu, da man na daɗe ina jiran lokaci ne, domin tun a baya na kan ɗan taɓa sin ɗaya zuwa biyu, kuma duk yawancin finafinan da na ke fitowa na Adam A. Zango ne; mafi yawanci shi ya ke saka ni.
 
“Amma dai duk a wancan lokacin ba a gani na a matsayin jarumi sai mawaƙi. Sai kuma a yanzu da lokaci ya zo ake yi mini laƙabi da Yawale Ɗankuma, don haka duk wanda ka ji ya kira ni da Auwal Ishaq, to tsohon sani ne.”
 
Yanzu akwai mutanen da su ke ɗauka cewar Auwal kurma ne. Ko yaya maganar ta ke?
 
“To gaskiya ni ba kurma ba ne,” inji shi. “Abin dai da na sani shi ne duk abin da ka saka ran ka a kan sa to za ka iya har ma ka fi yadda ake tunani. 
 
“Kuma ni mutum ne mai zuciyar na ga na samo abin da zan rufa wa kai na asiri, don haka duk abin da na saka kai na a kan zan iya zan yi ƙoƙari na ga na yi shi, kuma Allah zai ba ni damar na yi.
 
“Don haka tun da na ke a duniya ban taɓa yin rol ɗin ɗankurma ba, amma sai Allah ya ba ni damar da na zo na yi fice a cikin sa duk da ni ba kurman ba ne.”
 
Ko yaya rayuwar Auwal ta kasance bayan ya zama ɗankurma? 
 
Amsa: “To alhamdu lillah, tun daga lokacin da na zama Yawale Ɗankurma na ga nasarori ba zan ce ga iyakar su ba, domin a yanzu ba na samun hutu na tsawon sati guda ba tare da na samu gayyata ba.”
 
Dangane da soyayyar su da Rayya kuwa a cikin ‘Kwana Casa’in’, jarumin cewa ya yi:
“To su ‘yan kallo su na ɗaukar soyayyar kamar ta gaske ce, duk da ya ke shi ɗan kallo ka na yi masa uziri, domin duk abin da ya kalla, to ya gama yanke masa hukunci a waje ma haka ne, don haka ne ma ake cewa soyayyar mu da Rayya gaske ce ko a fili. Amma dai a zahiri ni da Rayya aminan juna ne, don haka babu soyayya a tsakanin mu.”
 
Daga ƙarshe, Auwal Ishaq ya yi kira ga masu kallon su da Rayya a matsayin masoya da su ɗauki abin a matsayin shiri kawai. 
 
Haka kuma ya yi masu fatan alheri, dangane da ƙaunar da su ke nuna masa.

Loading

Previous Post

Gidaje da mutane sun yi yawa a ‘Daɗin Kowa’, cewar Sallau

Next Post

‘Yan fim ba su san mutuncin kan su ba, inji Umar Inuwa

Related Posts

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Next Post
Alhaji Umar Inuwa

'Yan fim ba su san mutuncin kan su ba, inji Umar Inuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!