• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, July 28, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista ya yaba da zaɓen ƙungiyoyin IPI da NUJ, kuma ya yi kira da a yi aikin jarida yadda ya dace

* Ya taya Mojeed, Shekarau da Alhassan murnar lashe zaɓe

by WAKILIN MU
December 14, 2024
in Nijeriya
0
Minista ya yaba da zaɓen ƙungiyoyin IPI da NUJ, kuma ya yi kira da a yi aikin jarida yadda ya dace

Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI) da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) bisa nasarar gudanar da zaɓukan sababbin shugabannin su.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan ya taya murna ga Musikilu Mojeed, shugaban kamfanin jaridar onlayin ta Premium Times, da Ahmed Shekarau, Manajan Daraktan kamfanin Media Trust, kan sake zaɓen su da aka yi a matsayin Shugaba da Sakatare, bi da bi, tare da wasu jami’ai huɗu da aka sake zaɓa.

Ya ce: “Ina taya Malam Musikilu Mojeed, Shugaban kamfanin Premium Times, da Ahmed Shekarau, Manajan Darakta na Media Trust, waɗanda aka sake zaɓen su a matsayin Shugaba da Sakatare, bi da bi, da kuma sake zaɓen wasu jami’ai guda huɗu na IPI reshen Nijeriya.”

Ministan ya kuma yaba wa sauyin shugabanci cikin lumana da ake yi a NUJ, wanda ya haifar da zaɓen Malam Alhassan Yahaya a matsayin Shugaba da kuma Abimbola Oyetunde a matsayin mace ta farko da ta zama Mataimakiyar Shugaban ƙungiyar ta ƙasa.

Har ila yau, Idris ya yaba wa gwamnatin Jihar Imo saboda rawar da ta taka wajen gudanar da zaɓen na NUJ.

Ya ce: “Dole ne in yaba wa gwamnatin Jihar Imo kan goyon bayan da ta bayar da kuma karimcin ta wajen karɓar baƙuncin membobi da wakilan NUJ, wanda ya taimaka wajen samun nasarar zaɓen.”

Daga nan ya yi kira ga IPI da NUJ da su ci gaba da jajircewa wajen inganta aikin jarida yadda ya dace.

Ya ce: “A matsayin ku na masu kare gaskiya, dole ne ‘yan jarida su ba da fifiko ga gaskiya da riƙon amana a cikin aikin su. Ina kira ga ƙungiyoyin biyu da su tabbatar da cewa membobin su suna bin mafi kyawun ƙa’idojin aikin jarida don inganta dimokiraɗiyyar mu.”

Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da kare ‘yancin ‘yan jarida, inda ya ce, “Za mu ci gaba da kare haƙƙoƙin ‘yan jarida, ta yadda za a tabbatar da yanayi mai kyau don aikin jarida ya bunƙasa a Nijeriya.”

Ita dai Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya, wato International Press Institute (IPI), wata ƙungiya ce ta duniya da ke ƙunshe da ‘yan jarida, editoci, da shugabannin kafafen yaɗa labarai da suka himmatu wajen kare ‘yancin ‘yan jarida da inganta aikin jarida mai zaman kan sa da bambancin kafafen yaɗa labarai a duniya baki ɗaya.

Loading

Tags: Ahmed ShekarauInternational Press InstituteIPIMohammed IdrisMusikilu Mojeedzaɓe
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yi kira ga jihohi da kada su rushe Ma’aikatun Yaɗa Labarai

Next Post

Muna addu’ar Allah ya aurar da mu, inji jarumar Kannywood Hadiza Kabara

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
Muna addu’ar Allah ya aurar da mu, inji jarumar Kannywood Hadiza Kabara

Muna addu'ar Allah ya aurar da mu, inji jarumar Kannywood Hadiza Kabara

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!