SHUGABAN Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Katsina, Kwamared Lawal Rabe Lemo, ya yi kira ga Shugaban Kwamitin Shirya Babban Zaɓen Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Malam Bello Achida, da ya aje muƙamin sa saboda ana zargin sa da saka siyasa cikin harkokin ƙungiyar.
Lawal ya ce MOPPAN ba ƙungiyar siyasa ba ce.
Wannan kiran ya biyo bayan wata takardar zargi da ƙorafi wadda wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa manyan membobin MOPPAN ɗin ne suka rubuta ta, ta fara yawo a soshiyal midiya a daren jinya inda suka zargi Achida da sayar da mutuncin ƙungiyar ga masu harkar siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, musamman a babban zaben ƙungiyar da za a yi a watan gobe a Jihar Nassarawa.
Yahaya Bello dai ya yi takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2023, inda aka yi da Ƙungiyar Yahaya Bello Network (YBN) domin yi masa kamfen a Kannywood.
A yanzu tsohon gwamnan yana fuskantar shari’a bayan da Hukumar Yaƙi da Almundahanar Kuɗi (EFCC) ta maka shi a kotu kan zargin sace naira biliyan ɗaya daga asusun gwamnatin Jihar Kogi.
A makon jiya kotu ta ba da belin naira miliyan 500 gare shi bayan an tsare shi a gidan kurkukun Kuje, a Abuja.
Ita dai wannan takardar ƙorafin da ake wa Achida, tana ɗauke da kwanan wata 23 ga Disamba, 2024 kuma an rubuta ta ne ga Kwamitin Amintattu na MOPPAN wanda Alhaji Sani Mu’azu Makama yake shugabanta.
An nuna cewa an tura kwafen takardar, wadda babu sunayen waɗanda suka rubuta ta, ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa da Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya, da kuma Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Nijeriya.
Mujallar Fim ta samu kwafen takardar mai taken, “Koke Kan Yadda Ake Maida MOPPAN Jam’iyyar Siyasa ta Hanyar Ƙungiyar Yahaya Bello (Yahaya Bello Network, YBN)”, kuma ta fassara ta kamar haka:
“Zuwa ga masu daraja Membobin Kwamiti. Mu membobin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) da suka damu da abin da wanzuwa mun rubuto maku takarda ne domin mu bayyana damuwar mu dangane da abubuwan da ke faruwa a ƙungiyar mu a cikin ‘yan kwanakin nan waɗanda ke kawo barazana ga mutuncin ta da manufar ta.
“Mun lura da yadda ake ƙoƙarin juya MOPPAN zuwa jam’iyyar siyasa, aka fake da Ƙungiyar Yahaya Bello, wato Yahaya Bello Network (YBN).
“Alamar bayyanar wannan abin ban-tsoro ita ce a kwanakin nan aka riƙa kafa kwamitocin zaɓe waɗanda membobin su duk ‘yan ƙungiyar YBN ne, waɗanda suka haɗa da Ciyaman na Kwamiti, wato Bello Achida, da sauran membobi daga jihohin Neja da Yobe waɗanda su ne shugabannin YBN a jihohin su.
“Irin waɗannan abubuwan da ke faruwa, suna zagon ƙasa ne ga muradun dimokiraɗiyya da aka kafa ƙungiyar mu a kan su, kuma za su iya ture da dama daga cikin membobin mu waɗanda ba su yin tafiyar siyasar YBN.
“Kada mu manta da abin da ya faru a Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewa, Arewa Filmmakers Association, inda aka hana duk wanda ba ɗan YBN ba shiga zaɓe. Hakan ya jawo aka hana ɗimbin ‘yan fim ba da gudunmawar da suke so su bayar a harkar zaɓen ta hanyar dimokiraɗiyya a masana’antar su.
“Kwamitin tantance ‘yan takara da aka kafa kwanan nan, a bisa jagorancin mutumin da aka sani da ‘babban jagoran’ YBN, shi ma sai ‘yan YBN ya riƙa ba dama, wanda hakan ya ƙara saka damuwa a zukatan jama’a kan yadda aka yi fatali da muradun dimokiraɗiyya yake ƙara haifar da damuwa a cikin ƙungiyar mu.
“Mayar da MOPPAN ƙungiyar siyasa yana haifar da haɗurra da dama kamar haka:
1. Zubar Da Mutunci: An daɗe da sanin MOPPAN a matsayin lema mafi girma kuma wadda aka fi girmamawa a harkar fim a Arewacin Nijeriya. Alaƙanta ta da wata jam’iyyar siyasa zai rusa wannan darajar kuma ya zubar mata da mutunci a cikin masu ruwa da tsaki a harkar.
2. Hana Samuwar Mabambantan Ra’ayoyin: Ta hanyar bai wa membobin YBN muhimmanci a wajen samar da muƙamai da matakan yanke shawara, za mu fuskanci barazanar toshe bakin ra’ayoyi mabambanta a cikin jama’ar mu, wanda wata buƙata ce mai muhimmanci wajen samar da fasaha da ƙirƙira a wajen shirya fim.
3. Siyasantarwa: Idan aka bari aka saka MOPPAN cikin wata jam’iyyar siyasa, to an buɗe ƙofar a riƙa siyasantar da al’amuran ta kenan, inda duk wata shawara da za a yanke sai a dube ta a siyasance maimakon abin da ya fi alfanu ga industiri ɗin mu da masu cin abinci a cikin ta.
4. Hana Industiri Cigaba: Masana’antar shirya fim tana samun cigaba ne ta hanyar haɗin gwiwa da taimakekeniyar kowa da kowa. Siyasantar da al’amari kuwa yana toshe basira da ƙirƙira, wanda a ƙarshe za su hana samun faɗaɗa da cigaban Kannywood da ma harkar fim a Nijeriya baki ɗaya.
“Muna kira a gare ku da ku ɗauki matakin gaggawa domin bincikar waɗannan abubuwan da ke faruwa kuma ku tabbatar da cewa MOPPAN ta ci gaba da kasancewa ƙungiya mai zaman kan ta wadda ta sadaukar da kai ga tabbatar da cigaban harkar fim a Arewacin Nijeriya.
“Muna kira a gare ku da ku riƙe muradun dimokiraɗiyya, tare da rungumar kowa da kowa, da kare mutunci, ta yadda ƙungiyar mu za ta ci gaba da kasancewa yadda aka san ta.
“Idan kuwa har aka gaza wajen ɗaukar mataki kan waɗannan al’amurra, to sai mu yi tunanin cewa kuna goyon bayan abin da waɗannan shugabanni suke aikatawa wanda kuma a ƙarshe zai jawo barazana ga ɗorewar MOPPAN a hannun mutane waɗanda ba su damu da abin da ya fi zama alfanu ga industirin mu ba.
“Mun sa ido mu ga kun ɗauki matakin gaggawa kan wannan al’amari kuma muna fatar a samu maslaha wadda za ta kare mutunci da ɗorewar MOPPAN.
Mu ne naku, waɗanda abin ya shafa.”
Kwamared Lawal Rabe, wanda ke muradin takarar muƙamin Mataimakin Sakatare-Janar na Ƙasa na ƙungiyar a zaɓen MOPPAN da za a yi a watan gobe a Jihar Nasarawa, shi ne ɗan fim na farko da ya ce wani abu a kan wannan takardar ƙorafin.
A martanin da ya yi kan takardar, bayan buɗewa da Bismilla, sai ya ce: “Malam Ciyaman na Kwamitin Zaɓen MOPPAN na 2025, Bello Shehu Achida, lokaci ya yi da ya kamata ka yi murabus da kankin kan ka daga muƙamin ka saboda a samu damar yin bincike dangane da waɗannan zarge-zargen don a kare mutuncin wannan muhimmiyar ƙungiya tamu don Allah.
“Bayan haka, MOPPAN ƙungiya ce ta ƙwararru ba ta siyasa ba. Ba mu son a siyasantar da ƙungiyar mu.
“Bugu da ƙari, akwai buƙatar a shirya kuma a gudanar da ingantaccen zaɓe bisa adalci ba tare da saka hannun wani ba, wanda kowa da kowa a industirin fim ta Kannywood zai yi na’am da shi.
“Saboda haka, muna buƙatar matakin gaggawa na Kwamitin Amintattun MOPPAN a ƙarƙashin shugabancin Malam Sani Mu’azu Jos ta hanyar kwamitin da zai yi kyakkyawan bincike da tabbatarwa don a ba da sahihin rahoto kan waɗannan zarge-zargen da aka ambata.”
Sai dai Shugaban Kwamitin Amintattun MOPPAN, Alhaji Sani Mu’azu Makama, ya ci gyaran Kwamared Lawal Rabe da ya nuna masa cewa ba a bi ƙa’idojin rubuta takardar koke a wannan takardar ba.
Ya ce masa: “Alhaji Rabe, shin kai ne ka rubuta wannan koken? Idan haka ne, to don Allah ka faɗi duk wanda kake so ka tura wa ita, kuma ka rattaba hannu a kan ta don ta zama bisa ƙa’idar yadda ake yi.
“Idan kuma ba kai ne ka rubuta ba, to don Allah ka faɗa wa wanda ka samo ta a wajen sa cewa ya rattaba hannu kan waɗannan zarge-zargen yadda ya kamata sannan ya aika da ita yadda ya kamata.
“Na gode maka ƙwarai bisa fahimtar ka.”
Shi dai Bello Achida, an zaɓe shi ne a matsayin shugaban kwamitin zaɓen MOPPAN a cikin tsakiyar Oktoba da ya gabata sakamakon murabus ɗin da shugaban kwamitin na farko, wato Alhaji Bala Mu’azu Kufa ina, ya yi saboda wasu dalilai.
A ranar Lahadi, 8 ga Satumba, aka zaɓi Kufaina a muƙamin, amma ya aje aikin cikin wata ɗaya kacal.
Majalisar gudanarwar ƙungiyar ta maye gurbin sa da Achida bayan ta yi wasu gyare-gyare a cikin kwamitin zaɓen, misali ta rage yawan membobin kwamitin zaɓen daga 13 zuwa 7 kacal.
‘Yan kwamitin su ne Bello Achida (daga Sokoto), wanda shi ne mai riƙe da muƙamin babban mai binciken kuɗi (National Auditor); Malam Ibrahim L. Ibrahim (daga Jihar Nasarawa) mai riƙe da muƙamin Mataimakin Shugaba na shiyyar Arewa-maso-tsakiya a matsayin sakataren kwamitin zaɓe; Alhaji Abdul Mohammed Amart (wakilin furodusoshi); Hajiya Hadiza Mohammed (wakiliyar ‘yan wasa); da shugabannin jihohi a kowace shiyya ta Arewa, wato Ado Ahmad Gidan Dabino, shugaban MOPPAN na Kano (daga North-West); da shugaban MOPPAN na Yobe, Malam Khalifa (daga Arewa-maso-gabas); da kuma Alhaji Murtala Yakubu, shugaban MOPPAN na Jihar Binuwai (daga Arewa-ta-Tsakiya).