JAMILU Abdussalam, wanda aka fi sani da Jamil Hajaj, matashin ɗan kasuwa ne wanda ya mallaki kamfanoni kamar shida. Ya na gudanar da sana’o’in da su ka danganci sayar da kayan abinci da na sha (na dafawa da na ƙwalama) da sayar da kadarori kamar gidaje da filaye, da kayan fasaha da ƙere-ƙere, da kuma harkar nishaɗantarwa.
Jamil, wanda ya samu digirin sa ne a fannin yaɗa labarai (Mass Communication) daga Jami’ar Bayero, Kano, shi ne mamallakin manhajar Northflix wadda ake amfani da ita ana kallon finafinan Hausa. Wato maimakon mutum ya je kasuwa ya sayi fim, sai kurum ya sauko da manhajar a waya ko komfutar sa, ya riƙa biyan wasu ‘yan kuɗi kaɗan, don ya kalli finafinan da kamfanin Jamil ɗin ya ɗora a manhajar. Tunda kuma abu ne na intanet, kenan mutum zai iya kallon finafinan a ko’ina a duniya.
Babu shakka, manhajar Northflix kwaikwayo ce ta shahararriyar manhajar nan ta Netflix da ke Amurka wadda ake amfani da ita ana kallon finafinai da wasannin talbijin na Hollywood, Bollywood da Nollywood da na sauran ƙasashe.
A ranar 9 ga Yuni, 2020 manhajar Northflix ta cika shekara ɗaya cur da ƙaddamarwa a Kano. Tun daga kafuwar ta zuwa yanzu kuwa, ta kasance tsararriyar hanyar tallata finafinan Hausa a duniya ta zamani.
Domin jin yadda kamfanin Northflix ya kasance cikin tsawon shekara ɗaya ɗin nan, musamman manufar samar da shi da irin nasarorin da ya samu da kuma ƙalubale, da yadda Jamil ya ke hangen manhajar tasa a shekaru masu zuwa, mujallar Fim ta tattauna da shugaban kamfanin Northflix Nigeria Limited, wato Alh. Jamil Abdussalam (Hajaj), kamar haka:
FIM: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatun mu.
JAMIL HAJAJ: To, da farko suna na Jamilu Abdulsalam kuma ni ne shugaban kamfanin Northflix, kamfanin da su ke da manhaja ta yaɗa finafinan Kannywood ko na Hausa a faɗin duniya gaba ɗaya.
FIM: A yanzu, kamfanin ya cika shekara ɗaya da kafuwa. Za mu so ka yi wa masu karatun mu ɗan tsokaci kan nasarori da kuma matsaloli ku ka fuskanta a tsawon shekara ɗaya ɗin nan.
JAMIL HAJAJ: To alhamdu lillahi, nasarori dai za mu ce an samu, wanda a cikin nasarorin da mu ka samu shi ne, na ɗaya mun yi ƙoƙarin kawo gyararraki a kan wasu matakai guda uku waɗanda su ke kusan ginshiƙi da su ka sa mu ka shigo Kannywood. Waɗannan su ne, na ɗaya akwai maganar satar fasaha da ake ta koke-koke a kan ta; ta na ɗaya daga cikin matsalar da mu ka hango, kuma alhamdu lillahi mun tabbatar da cewa manhajar mu, duk wani furodusa idan ya ba mu fim ɗin sa, to lallai fim ɗin sa ba zai fita ba daga manhajar mu. To ka ga wannan matsalar mun magance ta.
Na biyu kuma akwai maganar yaɗa fim ɗin a fadin duniya gaba ɗaya, wanda a yau idan ka yi fim, maimakon a ce idan ka nuna a sinima a Kano babu inda za ka iya kaiwa kuma, in ka ce a sidi za ka buga mutane nawa ne masu DVD da za su kalla? Wannan matsalar sai mu ka ga ita ma za mu iya magance ta ta hanyar idan mai shirya fim ya ba mu mu ka saka a yau, duk inda mutum ya ke a faɗin duniya zai kalla. To ka ga wannan gagarumin cigaba ne, wanda an samu an yi.
To sai gaba ta uku, wadda ita ce inganta finafinan da ake yi, to ita ma ɗaya ce daga cikin matsalolin da mu ka hango, kuma yanzu a kan ta mu ke. Mu na ƙoƙarin mu ma mu fara yin finafinai da za mu gani sun kai inganci da ake tunanin su ne irin finafinan da ya kamata a ce su ne ake yi a Kannywood. Wannan a taƙaice su ne nasara.
Kuma alhamdu lillahi a yanzu za mu ce mu na da mutane sama da dubu sittin da su ke kan manhajar.
Na biyu kuma masana’antar Kannywood ɗin mun zo mun samu karɓuwa sosai da gaske, musamman a yanzu da wannan matsalar ta Covid-19 da ta shigo, mu za mu ce kamar nasara ce ma a gare mu. Ba don komai ba, a baya idan ka yi fim za ka kai ‘Film House Cinema’, to a yanzu duk wani waje, tun da wannan Covid-19 ya hana taro waje guda, manhajar Northflix kuma ta ba ka damar idan ka na da fim, za ka iya samun damar ka ɗora shi kuma mutum daga ɗakin sa ya kalla a kan wayar sa. To lallai kuwa ka ga wannan nasara ce babba kuma wanda mu na sa rai in Allah ya yarda da haka za a samu a kai gaci.

FIM: Su waɗannan finafinai da ku ke ɗorawa, ku na sayen su ne ko akwai wata yarjejeniya da ku ke yi da furodusoshi?
JAMIL HAJAJ: To wannan tsarin kamar guda uku ne, amma a yanzu gaɓar da mu ke kai ita ce ta sayen fim ɗin a wajen su. Idan sun yi fim mu zo mu kalli fim mu yi masa kuɗi. Amma ‘right’ ɗin mu ke saya, ba fim ɗin duka ba. To idan mu ka ga fim ɗin ya yi mana daidai da abin da mu ke so, sai mu ce, “To fim ɗin ka mun saye shi kaza.” To a kan wannan gaɓar mu ke.
Amma akwai lokacin da za mu zo ko mu kira furodusa ya shirya fim mu yi haɗaka mu shirya, ko kuma mu tsara shirya fim ya zamo namu ne na kan mu, yadda mu za mu sa kuɗi ɗari bisa ɗari wajen shirya fim ɗin. To wannan su ne tsare-tsaren da mu ke da su.
FIM: Wannan manhajar ana ganin kamar kwaikwayo ne da manhajar Netflix ta ƙasar Amurka, wanda su finafinai kawai su ke haskawa. To ita Northflix ta zo da wani salo na ɗora labarai na Kannywood. Ko me ya sa ku ka shigo da wannan salon?
JAMIL HAJAJ: Wato kusan yanayin kasuwancin ne. Kawai dai na ɗaya finafinai ne mu ke so mu tallata, kai ba ma finafinai ba, abubuwa wanda su ka shafi Arewa, don yanzu a shirye-shiryen mu, akwai labarai na abubuwan tarihin Kano da Arewa duk arewacin Nijeriya kamar maganar bambe, akwai tarihin sarakuna, da kuma tarihin shugabannin ƙasa, musamman waɗanda su ka fito daga Arewa. Don haka ba wai manhaja ce ta finafinai kaɗai ba, sai dai yanzu gaɓar nan da mu ka fara, da finafinai mu ka fara, har zuwa lokacin da za mu kai wannan gacin in-sha Allahu.
Batun maganar labarai kuma, labarai ba shi ne kusan muhimmin abin da mu ke yi ba, wato wata gaɓa ce da mu ka fara sai mu ka ga ai lallai ana buƙatar labarai, kuma mun fahimci cewar mutane daban-daban waɗanda su ke masana’antar, in abu ya faru, za ka ga ana ta yaɗa ji-ta-ji-ta, to kuma duk masana’antar babu wata kafa, to bari na je wadda in dai na ji labarin kaza, to zan tabbatar da labarin. To wannan shi ne dalilin da ya sa mu ka fito da tsarin, mu ka ce idan mu ka raine shi, nan gaba zai samu karɓuwa, wanda idan mutane su na jin ji-ta-ji-ta a masana’antar Kannywood, za su garzaya domin su tabbatar cewa lallai labari ne mai inganci.
FIM: Wanne irin shiri ka yi zuwa shekaru uku masu zuwa dangane da wannan kamfanin naka?
JAMIL HAJAJ: To kamar yadda mu ke faɗa wa kusan duka ‘yan masana’antar, Northflix cigaba ce ta kawo wa masana’antar, kuma cigaba shi ba ya zuwa a dare ɗaya, abu ne da har sai an raine shi da haƙuri da tattali da jajircewa har tsawon wasu lokuta. Lallai idan aka yi haƙuri, to zai haifar da ɗa mai ido.
Dalili kuwa shi ne, yanzu akwai misali kamar maganar a yanzu mu na da mutane kamar 60,000 da su ke sauke manhajar mu. Idan a yau aka yi haƙuri shekara ɗaya, biyu, uku, aka samu mutane kamar miliyan ɗaya, to idan mutane miliyan ɗaya su na saukar da manhajar mu (a kan kuɗi) 1,500, to ka ga za a samu kuɗi masu yawan gaske wanda kuɗin ko miliyan ɗari biyar ce ta ke yawo a masana’antar Kannywood, ba ƙaramin kuɗi ba ne. To amma kamar yadda na ke faɗa, sai an yi haƙuri, sai an haɗa kai gaba ɗaya mu da ‘yan masana’antar, mu yarda lallai cigaba ne mu ke so mu yi, to lallai mu na sa rai nan da lokaci na gaba Northflix za ta kawo gagarumin cigaba a Kannywood.
Amma dai kamar yadda mu ka faɗa, mu kaɗai ba za mu iya ba sai an haɗu da kowa da kowa.
FIM: A cikin shekara guda da kamfanin ka ya yi, yaya dangantakar ka da ‘yan masana’antar Kannywood ta ke, musamman ma furodusoshi?
JAMIL HAJAJ: Magana ta gaskiya, akwai dangantaka mai kyau, kuma alhamdu lillahi, tunda lokacin da mu ka fara, da yawa sun ba mu finafinan su ma ba tare da mun biya ba, kuma har mu ka zo mu ka fara biya mu na warwarewa. To akwai wannan dangantakar. To amma ka san shi abu sabo, ba kowa ya ke da saurin karɓar sa ba. Idan ka zo da sabon abu, wasu sai sun ta juya shi, su ga ta wacce gaɓa za su shigo. To wannan ita ce. Kuma ba za ka ga laifin su ba, domin shi sabon abu, ba za ka rufe idon ka ba ka shiga.
Mu na sa rai dai nan da wasu lokuta waɗanda ba su karɓe mu ba ma za su karɓe mu, waɗanda su ka karɓe mu kuma za mu ƙara haɗa ƙarfi da ƙarfe domin Northflix ta kai gaci.
Babban abin da mu ke faɗa kullum shi ne Northflix cigaba ce ga masana’antar Kannywood da ma Arewa gaba ɗaya, wanda idan Allah ya sa ta karɓu, lallai lallai ba ƙaramin jihadi za mu yi ba wajen yaɗa abubuwan da Arewa ta ke yi a duniya. Mutane wadanda ba su da damar zuwa Arewa kuma ba sa kallo a satilayit, sun samu damar samun abubuwan da za su kalla daga Arewa, wanda kuma cigaba ne ga Arewar.
FIM: Daga ƙarshe, menene saƙon ka ga ‘yan fim da su masu kallo?
JAMIL HAJAJ: To na farko dai ga ‘yan fim ɗin: na faɗa na ƙara faɗa, lallai ‘yan fim mu zo mu haɗu mu yi wa Northflix rubdugu. Na san wasu za su faɗa su ce ai idan aka yi, wasu aka yi wa! To ko da wasu aka yi wa, a hankali wata rana za ka ga kai aka yi wa, domin abin da Northflix za ta samu, ba ita kaɗai za ta ci ba, za ta kawo kuɗin ne ta danna a masana’antar domin a ƙara yin wasu finafinan. Don haka lallai lallai cigaban Northflix cigaban masana’antar ne. Idan mun rufe ido mun kwashi kuɗi masu yawan gaske mun zo mun danna, kafin a samu waɗanda za su zo su yi wannan jajircewar na abin da mu ka yi, to aiki ne, tunda masana’antar ta na nan a tsaye tsawon shekaru kafin mu zo, babu wanda ya yi. Don haka idan ‘yan masana’antar cigaba ake so, lallai a zo mu haɗu a ga menene ake buƙata na cigaba.
Kuma za ta iya yiwuwa Northflix ta zo ta yi kurakurai. To lallai idan aka yi, akwai shugabanni da ya kamata su kira su ce lallai a kan gaɓar nan ba haka ya kamata ku yi ba, mu ma a kan haka za mu ce ga inda mu ke tunani, a gare mu shi ne gyara. To idan aka tafi a haka, za ka ga an samu cigaban da ake buƙata.
To kuma su masu kallo babu abin da za mu ce sai dai sambarka. Gaskiya mutane da yawa su na bibiyar manhajar Northflix. Ana samu a yi kallo. Da man shi mai kallo babu abin da ya ke so sai dai ka yi fim mai kyau ka ba shi. Yanzu mutane su na kai fim ɗin su YouTube. Wataƙila za ka kai ka ɗan samu abin kashewa, amma cigaba, YouTube ba za ta ba ka cigaba ba. Lallai in ka na buƙatar cigaba ne mai ɗorewa, to Northflix ce za ta ba ka wannan cigaban, domin kuwa wataƙila yanzu ba ka samu riba ba. Amma kai-tsaye Northflix ta na iya ɗaukar kuɗi kai-tsaye ta ba ka domin ta saki fim. To idan mu na rainar ta, idan a yanzu mu na sayen fim dubu ɗari biyar, miliyan ɗaya, lallai-lallai akwai lokacin da za a rinƙa sayen fim har naira miliyan hamsin, to ka ga kuwa cigaba ne. Don haka ina kira ga masu kallo da cewa su ƙara ba mu goyon bayan da su ke ba mu, mu kuma za mu ci gaba da inganta musu aikin mu domin samar musu da abubuwan da za su kalla masu ƙayatarwa.
Don haka a kullum mu na farin ciki da irin goyon bayan da mu ke samu daga gare su.
FIM: To madalla mun gode.
JAMIL HAJAJ: Ni ma na gode.
![]()







