• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, May 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwarzo Maitama Sule

by DAGA KHALID IMAM
July 3, 2020
in Marubuta
0
Alhaji Yusuf Maitama Sule (1927-2017)

Alhaji Yusuf Maitama Sule (1927-2017)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
(Waƙar tunawa da Jakada Yusuf Maitama Sule Ɗanmasanin Kano, 1929- 2017, wanda a yau ya cika shekara uku cif da rasuwa a ranar 3 ga Yuli, 2017)
 
 
Maitama Sule jarumi,
Shi Ɗanmasanin Kano ne
Yai jakadancin yabawa,
Gwarzo a cikin gwaraza,
Haziƙi ne mai fasaha,
Hikimar zance wajen sa,
Duk Arewa ina kamar sa?
 
Na tabbata duk ƙasa rmu,
Har Afrika bai da tsara,
Shi mai kishin ƙasa ne,
Kuma mai kishin Arewa,
Ya yi kishin ya yi aiki.
 
Yai ƙwazo don baƙaƙe,
Je ka duba kai aboki,
Lokacin da ya ke a UN,
Shi ya kewaya duniya kaf,
Don baƙaƙe ‘yan Afrika,
Ko Mandela mu duba,
Ƙoƙarin sa ya ba shi ‘yanci,
In da mai ja babu shakka,
Ilimin sa ya na da rauni.
 
Maitama ai malami ne,
Na addini da boko,
Ɗan siyasa ne fa tammi,
Shi da Sardaunan Arewa,
Sun yi yaƙi don mu rayu,
Mui mutunci mu Arewa.
 
Can a Legas ya yi fama,
Don ƙasar mu ta kama hanya,
Har ta kere duk ƙasashe,
Na baƙaƙe har farare.
 
Maitama tushen karatu,
Na manya ne garin mu,
A Kano jama’a mu lura,
Ɗaliban sa akwai mazaje,
Sun yi NEPU su ‘yanta kowa,
Tanko Yakasai da Mudi, 
Sha’iri ne shi Sipikin,
Ɗalibai ne gun sa Yusuf.
 
Maitama mai gaskiya ne,
Ba shi yin ƙarya a so shi,
Bai da ƙyama ba shi ɓaci,
Shi mutum ne mai salama,
Mai mutunci mai adala,
Bai fushi kuma ba shi gaba.
 
Ɗan jarida ne cikakke,
Ɗan dirama ne haƙika,
Cibiya ta Kano Arewa,
Har ƙasar Nijeriyar mu,
Ya na gaba gun su rayu,
Bai da gandar zaga dangi,
Don matasa ‘yan Arewa,
Duk su tashi su kama ƙwazo,
Su bar barci da ganda,
Kar a bar mu a baya komai.
 
Maitama Sule ya yi nisa,
Duniya ta san shi ainun,
Garkuwa ne shi fa Yusuf,
Bai yarda da murɗiya ba,
Zalunci in fa an yi,
Bai shiru ko yai burus ba.
 
Tarihi ya fa san shi,
Ya ƙware sosai fa Yusuf,
Haziƙi ne gun karatu,
Jami’o’i sun fahimci,
Ƙoƙarin sa da haziƙanci,
Da yawa sun karrama shi,
Sun ce ɗa ne halali,
Wanda ke kishin ƙasar sa.
 
Masarauta babu shakka,
Ta Kano tai rashin ɗa,
Mai azanci mai zalaƙa,
Mai balaga ko a zance,
Maganar sa ta na da zaƙi,
Ko zuma da rake haƙiƙa,
Ba su kai maganar sa zaƙi,
Ga amfani ga kowa.
 
Duniya duka na karaɗe,
Ni kamar sa a zihir sam,
Babu shi ko ban faɗa ba,
Domin shi bai da ganda,
Aiki duk nasa zai yi,
Ko naka idan ka ce zo,
Ɗan kama min na ɗora,
Zai sa hannu ya kama,
Ya aza ma don ka ɗauka.
 
Ƙaddara da ta sami Yusuf,
Hannu biyu shi ya amsa,
Har ya gode wa Ilahu,
Ni’imar sa gare shi kullum,
Rabbu ne mai jarrabawa,
Mai bada gani da ji du,
Jarrabawa yai wa Yusuf,
Ya janye ganin sa tabbas,
Babu raki babu kuka,
Godiya yai tai wa Allah,
Har ran da ya tai gare Shi.
 
Shi aboki ne na kirki,
Malami ne shi ga Sarki,
Ado Ɗan Abdu zaki,
Hadari mai nashe birni,
Shi ruwan sha ne mu lura,
Mai amfani ga gona,
Mai sa shuka yabanya,
Tai kore shar abin ta,
Ranar girbi a ɗiba,
A kai rumbu a tara.
 
Maitama wallahi Allah,
Shi rumbu ne na ilmu,
Tarihi ma gwani,
Baitoci sai ya rera,
Ko lacca in ya yi ta,
Jinjina da yabo anai mas,
Baiwa ce Rabbu yai mas,
Ta zalaƙa ga balaga,
Iya saƙa batu a ji shi,
Zuciyar jama’a ya ratsa,
Maitama Sule ɗan Kano,
Yolawa Unguwar su.
 
Hadimi ne shi ga Sarki,
Sutura Allahu yai mai,
Na abokai har da ‘ya’ya,
Shi ƙusa ne a birni,
Tun Arewa ana ta barci,
Don jigo ne Arewa, Maganar sa ta na da ƙarfi.
 
Tauraron ɗa ga Abba,
Ya haske sama’u tabbas,
Shugabannin soja na ji
Sun yi biko nai da safe,
Domin hanya ya nuna,
Jagoranci su gan shi,
Kuma sui koyi da gwarzo.
 
Shugabanni ‘yan siyasa,
Shi taska ne wajen su,
In sun rikice a mulki
Ba su ganda sai su rugo,
Nan wajen sa su nemi hanya.
 
Ko ƙasar Kamaru da Nijar,
Ba su yin sanya su rugo,
Har Kano domin su gan shi,
Hanya da ƙayar da sun bi,
Nan take ya ce su bar ta,
Da duhu da ƙaya a hanyar.
 
Bai saci kuɗin ƙasa ba,
Ya tafka gida a Landan,
Yai ministan mai na farko,
Bai washe kuɗin ƙasa ba,
Shi ƙasar sa kawai ya duba,
Bai matashin kai gida,
Dukiyar jama’ar ƙasar sa,
Ya kwashe yai Amurka,
Ya ɓoye yai bushasha.
 
Hidima da yawa haƙiƙa,
A Kano da ƙasa Arewa,
Ya yi su ƙwarai da himma,
Ko a birni ko a ƙauye,
Je Abuja je ka Legas,
In ka so je ka Paris,
Duk an san ɗa ga Abba.
 
Ya Ilahu ka dubi Yusuf,
Rahamar ka ba shi Allah,
Shi Ɗanmasani mu duba,
Bai ɗagawa shi ga kowa,
Allah domin Aminu,
Gafarar ka ka yi wa Yusuf,
Domin kam ya bi Abba,
Duk wanda ya so mahaifa,
Ya bi su cikin biyayya,
Bai taɓewa haƙiƙa.
 
Ɗan Abba ya na da kirki,
Shi mutum ne mai amana,
Bai mantawa da khairan,
Kafin rai yai halin sa,
Shi yai hidima ga ‘ya’yan,
Tafawa Ɓalewa gwarzo.

Loading

Previous Post

Manhajar Northflix cigaba ce ga Kannywood – Jamil Hajaj

Next Post

Haɗari: Jarumar Kannywood Khadija Kyari ta sha da ƙyar

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Khadija Kyari da filasta a fuskar ta. A dama kuma jar motar da ta faɗi da su ce

Haɗari: Jarumar Kannywood Khadija Kyari ta sha da ƙyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!