AN bayyana ilimi a matsayin matakin farko na samun cigaba a masana’antar finafinai ta Kannywood.
Haka kuma an nuna cewa matuƙar babu ilimi, to ba inda harkar fim za ta je illa ta yi ta komawa baya kamar yadda ake gani a yanzu.
Wani matashi a masana’antar, Abubakar H. Kura, shi ne ya bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da ya yi da mujallar Fim dangane da halin da masana’antar ta samu kan ta a ciki a yau.
Abubakar ya kasance mai yin sana’o’i da yawa a masana’antar, kama daga matsayin darakta, furodusa, marubucin labari har zuwa mai ɗaukar hoto.
A hirar, ya ce dole ne masu kishin harkar da ma waɗanda su ke so su ci gajiyar masana’antar su tashi tsaye su nemi ilimin da zai inganta sana’ar tasu.
“Don haka ne ni a karan kai na na tashi na bazama neman ilimi domin na tsira da rayuwa ta,” inji shi.
Abubakar ya ƙara da cewa, “A yanzu na gama jami’a, ina kan tsarin yi wa ƙasa hidima, don haka ne ma a yanzu ba a gani na sosai.
“Duk da ya ke dai karatun da na yi bai shafi masana’antar finafinai ba kai-tsaye, saboda abin da na karanta ya shafi tsara taswirar gini ne kamar gida ko wata masana’anta wanda tsarin karatun nawa lissafi ne tun daga kan tsara taswirar gida tun daga fili har a gama fentin zuwa shiga. Amma dai idan mu ka ɗauke shi ta wani ɓangaren, ya ɗan danganci harkar fim, kamar za a iya cewa in za a gina wani waje da za a yi aikin fim a ciki to ka ga a nan aikin mu ya shigo.
“Don haka ta wani ɓangaren, zan iya tafiyar da karatu na a cikin harkar fim yadda mutane za su bada zanen gida da kuma tsarin da za a yi.”
Ganin cewa ya kusa kammala yi wa ƙasa hidima, ko ba ya ganin idan ya gama zai ga kamar ya fi ƙarfin ya yi aiki a masana’antar? Sai ya amsa, “To ai ka san mutum ba ya manta mafari, don haka ni ina ganin duk mutumin da ya ke Kannywood idan an ce ya fita to a tunani na bai fita ba ne, ya koma gefe ne kafin ya dawo. Don kamar harkar siyasa ce; ɗan siyasa ba ya dainawa, don haka ba a daina fim. Ko ya samu kuɗi a wani ɓangaren, zuwa zai yi ya zuba su a masana’antar.

“Don haka na ke bada shawara ga abokan sana’a ta da cewar su yi ƙoƙari su koma karatu, a samu dai ko yaya na riƙe takardar kammala karatu, domin ta dalilin wannan takardar sai ka ga ka samu wani ƙarin cigaba a rayuwa.
“Amma idan ba ka da shi, haka za ka gani za a samo wani a ba shi, wanda bai ma kai ka ƙwarewa ba.
“Kamar ni yanzu, ka ga na yi karatu ne ba da niyyar na yi aikin gwamnati ba, amma ina zaune sai Allah ya kawo wani ya nemi ma’aikaci, na kai takarda ta, na fara aiki na wucin-gadi kafin na tafi hidimar ƙasa. Ka ga duk da haka ban bar masana’antar ba, sai ma ƙara nemo mata hanyoyin cigaba na ke yi yadda za ta bunƙasa.
“Don haka abu ne mai kyau ‘yan fim su tashi su nemi ilimi domin kare rayuwar su da ta masana’antar su. Kuma ina fatan hakan zai zama izina ga dukkan ‘yan fim da su ke cikin harkar da ma waɗanda sai nan gaba za su shigo.”