SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai Da Dab’i ta Jihar Kano, Malam Isma’ila Na’abba (Afakallah) ya yi kira ga gidajen rediyo da ke watsa shirye-shiryen su a Kano da su kiyaye sabuwar dokar nan ta samun izinin hukumar a kan duk wata waƙa da aka yi da nufin yabon Manzon Allah (s.a.w.).
Ya ce dokar, wadda ke bada lasisi da kuma neman izini ga duk sha’irin da ke so ya yi waƙar yabon Manzo ko ya gabatar da majalisi a jihar, ta na nan daram.
Afakallah ya bayyana haka ne a lokacin wani taro da ya yi da gidajen rediyo da ke Kano a jiya Laraba, 15 ga Yuli, 2020 a ofishin hukumar da ke Titin Maiduguri a birnin na Dabo.
Shugaban ya ce, “Ba za mu zuba ido mu na kallo ana kalaman ɓatanci ga Allah da Manzon sa tare da zagin shaihunnai ba, irin yadda wasu su ke yi da sunan waƙoƙin addini, wanda kuma hakan ke kawo barazana ga zaman lafiyar da mu ke da shi a Jihar Kano.”
Ya ci gaba da cewa: “Ba a hana ka yi waƙa ba, amma ya zama dole ka kiyaye doka da martabar Allah da Manzon sa da kuma bayin Allah nagari.
“A don haka daga yanzu ba za mu yarda wani da sunan waƙa ya fito ya na kalaman ɓatanci ba. Saboda haka mu ka saka dokar duk wani da zai yi majalisi a faɗin Jihar Kano sai ya zo ya nemi izini, an gamsu da abubuwan da zai faɗa da kuma irin taron da zai shirya don kauce wa faɗa tare da zubar da jini kamar yadda wasu lokuta su ke faruwa.
“Sannan daga yanzu babu wani sha’iri da zai saki waƙa, dole sai ya kawo Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta duba ta yarda da ingancin abubuwan da zai ya furta.
“A kan haka za mu kafa kwamitin da zai duba tare da tace waƙoƙin da sha’irai su ke yi. Don haka ma za mu samar da malamai masana shari’a da waƙoƙin Musulunci da za su yi taron tantancewar.”
Afakallah ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai, musamman ma na Kano, da su bayar da tasu gudunmawar ta hanyar kauce wa saka waƙoƙin da ba su samu tantancewa ba, domin ta haka ne za a samu damar magance matsalolin da ake samu na yin waƙoƙin da su ka saɓa da fahimta, wanda hakan ne ya ke kawo tashin hankali, “har ma a yanzu an fara ƙone-ƙone wanda in aka zuba ido nan gaba ba a san abin da zai faru ba.”

Bayan kammala jawabin nasa, wakilan hukumomin tsaro da su ka haɗa da DSS, ‘yan sanda da Hukumar Hisbah da su ka halarci taron sun nuna goyon bayan su tare da ƙudurta yin aiki da hukumar sa don magance matsalar.
A cewar su, a yanzu lamarin ya yi yawa ta yadda har an kai ga ƙone-ƙone da yunƙurin ɗaukar fansa, wanda kuma idan aka bar abin a haka nan gaba ba a san abin da zai faru ba.
Su ma wakilan mawaƙan da su ka halarci taron sun nuna goyon bayan su ga matakin da hukumar ta ɗauka domin kawo gyara a kan al’amarin.
An dai yi taron an tashi lafiya ba tare da an samu wani ƙorafi daga wakilan mawaƙan ba.
