A YAU al’amura sun ƙara lalacewa, tarbiyya ta yi ƙaranci, sharholiya ta yawaita a ko’ina, fyaɗe, luwaɗi, zinace-zinace da tambaɗewa kullum ƙaruwa su ke. Babban dalili na na yin wannan rubutun shi ne don nemo hanyoyin da za mu gane inda matsalar ta ke don sanin yadda za a kawo gyara a kan ta wajen kula da rayuwar ƙananan yara maza da mata masu tasowa a wannan zamani da mu ke ciki a wannan ƙasa tamu ta Nijeriya.
DALILAN LALACEWA
1 – Sakaci, kwaɗayi, jinkirin aure, fin ƙarfin iyaye, da miyagun abokai su ne manyan masu kawo wannan matsalar.
2 – Rashin sa ido da kula daga unguwanni da sakacin iyaye wajen lura da sa ido sosai kan ‘ya’yan su, sannan kuma ko-in-kula da irin mazan da ‘ya’yan su ke kulawa ko mu’amala da su.
3 – Talace-tallace. Yara ƙanana mu na ganin cewar tallar su talauci shi ya ke kawo ta saboda neman yadda za a tsira da rayuwa. Wasu daga ciki ko makaranta ba sa samun damar zuwa saboda yanayin da su ke ciki tare da iyayen su, sannan wasu yaran su na zuwa makaranta amma da zarar sun dawo za su ɗauki kayan talla don samo yadda za su biya buƙatun su na yau da kullum.
Babban abin da na ke so na nuna a nan shi ne mace za ta ɗauko tallar naira ɗari biyar amma wani zai ba ta dubu ɗaya ya ce ta raba wa yara abin da ta ke sayarwa, haka gobe ma zai neme ta ya biya buƙatar sa a kan kuɗin da zai ba ta ta koma gida ko ta je ta sayi kayan sawa sannan ta ci abin da ran ta ya ke so na more rayuwa wanda iyayen ta ba za su iya saya mata ba.
4 – Rashin jan ‘ya’ya mata a jiki tare da yawan ba su shawara, jan hankali da nuna damuwa da su da mafiya yawan iyaye ba sa yi.
5 – Tsadar rayuwa, talauci da yunwa tare da rashin galihu na taimakawa sosai wajen taɓarɓarewar tarbiyya.
SHAWARWARI DON SAMUN MAFITA
1 – Ya kamata iyaye su sanya ido sosai a kan ‘ya’yan su, ƙanana da manyan. Ko’ina yarinya za ta je, a haɗa ta da ɗan rakiya (ƙanin ta mai ɗan wayo) saboda ‘ya’ya mata sai da linzami, in ba haka ba kuma sai su tsallake inuwar su su faɗa rana da iyayen su.
2 – Karantar halaye, ɗabi’un ƙawaye da abokan hulɗar su.
3 – Samun jaurar da ba sai ta yi nesa da gida ba wajen talla.
4 – Idan aka samu ciki kuma aka gano wanda ya yi cikin, to sai a ɗora masa nauyin ɗawainiyar ta tun kafin haihuwa har bayan haihuwar ta. Sannan kuma idan ta gama shayarwa sai a ba shi ɗan sa.

5 – Akwai buƙatar wayar da kan al’umma kan illa da hatsarin da ke cikin irin wannan harkar. Misali:
√ – hanya ce mafi sauƙi wajen kamuwa da cututtuka irin su ƙanjamau;
√ – ɗaukar cikin shege;
√ – shiga wahala da ƙunci tare da kunyar fita da yin wargi cikin al’umma;
√ – zubar mutunci da faɗuwar girma tare da samun mummunar shaida a cikin al’umma;
√ – samun mai auren ta zai yi matuƙar wuya, ko ta samu ma sai dai na je-ka-na-yi-ka;
√ – tafiyar budurci tun a dandali.
6 – Ya kamata iyaye su riƙa kula da irin shigar banzar da ‘ya’yan su su ke yi tare da ɗaukar matakin hana su.
7 – Ya kamata shugabanni su riƙa tura masu irin wannan laifin gaban alƙali don yanke hukunci.
8 – Limamai, malamai shugabanni, kafafen sadarwa, iyaye, da sauran mutanen gari a tashi tsaye sosai wajen wayarwa da sa ido kan wannan al’amarin da ke faruwa a gari.
9 – Ɗaukar matakin ba-sani-ba-sabo kan duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Misali, idan shugaba ne ko jagora a ƙwace matsayin sa; idan kuma baƙo ne to a kore shi, idan kuma ɗan gari ne to ana iya yi masa hukuncin ɗauri bisa shari’a.
10 – Auren Wuri abu ne mai kyau, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake samun yawan lalacewar ‘yanmata ta hanyar zinace-zinace da su ke yi. Rashin aure ke janyo hakan a cikin wasun su.
Allah ya shirye mu, ya shirya mana zuri’a, ya ƙara sanya mana ƙyamar aikin assha.
![]()






