Arc. Ahmad Musa Ɗangiwa
Literary Competition 2019
(Gasar Gajerun Labaran Hausa)
RAHOTO DANGANE DA TARON BITAR DA AKA YI TA MUTANE 30
WANDA AKA GUDANAR A MUNAJ EVENTS CENTRE, KATSINA, A RANAR 15 GA AGUSTA, 2020
AN fara yi wa gwarazan gasar su 30 rajista wanda Malam Mustapha Kabir ya yi, inda kowa ya rubuta sunan sa lambar wayar sa da sunan labarin sa, da jihar sa. An kuma raba wa mahalarta taron littafi, ‘face mask’, biro, jakunkuna duk masu ɗauke da tambarin gasar.
Kabir Sa’idu Bahaushe ne kakakin taron. Bayan gabatar da manyan baƙi, an ba kowa damar gabatar da kan sa da labarin sa.
Daga nan shugaban taron, Yazid Nasudan, ya yi taƙaitaccen jawabin buɗewa.
Daga nan ne kuma ‘yan taro su ka saurari jawabi daga manajan bankin bada lamuni, reshen Jihar Katsina, Alhaji Rabi’u Ali, a kan bada lamunin gina gidaje na ƙasa.
‘Yan taro sun karya kumallo, daga nan aka yi tambayoyi dangane da bankin bada lamunin gina gidaje na ƙasa.
Malam Hamza S. Usman ya gabatar da jawabi a kan abin da ya kamata marubuci ya kula da su kafin labarin sa ya cika sharuɗɗan nazari.

Bayan gama jawabin sa, an ba masu sauraro damar su yi tambayoyi game da jawabin da Malam Hamza ya gabatar.
Injiniya Suraj Yazeed Abukur, Manajan Daraktan hukumar kula da hanyoyi ta Jihar Katsina (KASROMA), ya gabatar da maƙala a kan abubuwan da ya kamata marubuci ya lura da su yayin da ya ke magana a kan matsalolin gine-gine. Jawabai ne ya yi waɗanda duk marubucin da zai yi labari a kan gini tabbas ya na buƙatar su, matuƙar dai ya na son ya yi rubutu mai inganci.
Shi ma kamar na baya, ‘yan taro sun yi tambayoyi a kan abubuwan da ba su gane ba ko su ke son sani game da jawabin da ya yi. An yi tambayoyi masu ma’ana kuma ya amsa.
Ado Ahmad Gidan Dabino ya gabatar da maƙalar sa “Matakan Rubuta Gajerun Labarai”, wadda ta ƙunshi menene gajeren labari? Yadda ake rubuta ƙayataccen labari bisa doron matakai, inda har ya kawo wasu matakai guda bakwai da duk marubucin da ke son labarin sa ya inganta ya kamata ya bi.

‘Yan taro sun yi tambayoyi, kuma sun samu gamsasshiyar amsa.
Daga nan aka ci abincin rana, aka ba mahalartan su 30 satifiket da kuɗaɗe waɗanda za su riƙe.
* Zaidu Barmo shi ne jami’in yaɗa labarai na kwamitin shirya gasar
“Arc. Ahmad Musa Dangiwa Literary Competition 2020”
![]()






