• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shekara a kujera: Minista Sadiya ta jinjina wa ‘yan jarida da ma’aikatan agaji

by DAGA WAKILIN MU
August 22, 2020
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MINISTAR Harkokin Agaji Da Jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Faroukh, ta yaba da ƙoƙarin kafafen yaɗa labarai, ma’aikatan agaji da hukumomin haɗin gwiwa a daidai lokacin da ma’aikatar ta ta cika shekara ɗaya da kafawa.
 
Ita dai wannan ma’aikata, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙirƙire ta a ranar 21 ga Agusta, 2019 domin aiwatar da manufofi da ayyukan agaji, da rigakafin aukuwar bala’o’i tare da kai agajin gaggawa, sa’annan da gudanar da aikace-aikacen taimaka wa jama’a mabuƙata.
 
A cikin wata takardar sanarwa da mai agaza mata a harkar aikin yaɗa labarai Halima Oyelade ta raba, ministar ta yi la’akari da cewa “wannan shekara ce da aka yi abubuwa da dama, mai cike da ƙalubale da abubuwan sha’awa wadda a cikin ta mu ka koyi hanyoyin kai agaji ga jama’a da kula da bala’o’i, amma a duk cikin ayyukan mun maida hankalin mu wajen cika aikin da aka ba mu wanda ya ƙunshi kai wa jama’a ɗauki, hana aukuwar bala’i tare da agaza wa waɗanda bala’i ya auka mawa, da kuma fito da hanyoyin rage raɗaɗin bala’i idan ya faru, wanda hakan ya taimaka mana wajen inganta aikin mu saboda nan gaba.”
 
A lokacin da ta ke yaba wa Shugaban Ƙasa a kan hangen nesa da ya yi na ƙirƙiro ma’aikatar wadda ta kasance kan gaba wajen yaƙi da annobar korona, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta gode masa saboda ɗora ta a kujerar direbar ma’aikatar da ya yi.
 
Haka kuma ta yi la’akari da cewa a cikin wannan shekara ɗayan, ta koyi muhimman darussa tare da samun sabuwar fahimta game da hanyoyi masu ɓullewa da marasa ɓullewa a wannan aiki.
 
Yayin da ta ke yaba wa kafofin yaɗa labarai, ministar ta ce waɗannan kafofi abokan tafiya ne waɗanda tilas ne a haɗa ƙarfi da su don samun nasara. 
 
Ta ce, “Ina so in bayyana maku a yau cewa aikin da ku ke yi ya dace.”
 
Ta ce da yake ba hurumin ta ne ta bai wa kan ta maki kan nasarorin da ta samu ba, amma a shirye ta ke ita da abokan aikin ta za su ci gaba da aikin su a cikin sadaukarwa da jajircewa don cika alƙawurran aikin su, wanda ya yi daidai da jigon cikar su shekara ɗaya – wato Service2Humanity.”
Ministar ta yi jinjina na musamman ga “ma’aikatan agaji da kuma abokan haɗin gwiwar mu a wannan sashe daga hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya irin su OCHA, IOM, UNHCR da Hukumar Abinci ta Duniya, Bankin Duniya, USAID da Tarayyar Turai (EU), da kuma sauran hukumomin haɗin gwiwa waɗanda su ka ci gaba da bada agaji duk da halin rashin  tsaro da ake ciki da kuma wahalhalun da su ke fuskanta.
 
Ta kuma yi jaje kan waɗanda su ka rasu a wuraren da ake da rashin tsaro a cikin wannan shekara ɗayar da ta gabata.
 
Ministar ta yi bayanin cewa cika shekara ɗaya da ƙirƙiro ma’aikatar ya sa tilas su dage sosai.
 
Ta ce, “A yayin da mu ke murnar cika shekara ɗaya, ina so in ce lokaci ya yi da ya dace mu sake zage dantse wajen aiwatar da aikin mu. Dole ne mu nemo hanyoyin da za mu faɗaɗa aikin kula da bala’o’i, samar da agaji da kuma fito da hanyoyin tallafin jama’a wanda hakan zai taimaka mana wajen inganta aikin mu a nan gaba.”

Loading

Previous Post

Gasar Ahmad Ɗangiwa: An yi wa zakaru 30 bita

Next Post

Mu daina ɓata wa Musulunci suna

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Wasu mata Musulmi a lambun hutawa

Mu daina ɓata wa Musulunci suna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!