A CIKIN ƙasa da shekara guda na samu kyasa-kyasai fiye da goma na matan da aka auro su aka musulantar da su daga wasu shiyyoyi na ƙasar nan zuwa Arewa, amma su na cikin tsanani da tashin hankali da yawan su ma an sake su ba su da gurin zuwa saboda sun rabu da iyayen su da dangin su da garin su saboda wanda su ka musuluntar da su su ka aure su.
Na jima ina son yin rubutun nan saboda lamarin ya na ɓata min rai matuƙa ina janyewa, saboda ban fiye son yin maganar da ta shafi addini kai-tsaye ba saboda bambanci ra’ayi. Amma wannan lamarin na neman janyo mana babban ƙalubale game da musuluntar da wasu.
Babban tashin hankalin shi ne su matan da ake aurowar sai sun fara tara yara sannan su ke samun wannan matsalar.
A jiya wata da ta kira ni ta na ba ni labari bayan ta musulunta ta sha azaba a hannun iyayen ta matuƙa, amma haka ta jure har ta janyo ƙanwar ta ta musulunta ta auri Musulmi, amma su duka biyun auren su ya mutu, sun koma garin su saboda wahalar da su ke fuskanta a nan, amma dangin su sun ƙi taimaka masu saboda sun musulunta. Su na cikin tsananin wuyar da su kan yi sati ba su ci abinci ba sai kame-kame, kuma su na ganin ana taimaka wa sauran ‘yan’uwan su da ba su musulunta ba, ana cewa idan su na son a taimaka masu sai dai su bar Musulunci. Ta ce min wallahi wahalar da su ke sha zuciyar su ta fara karaya yanzu. Na ce su taho Kano zan kama masu haya na ba su jarin sana’ar yin abinci da su ke yi a can baya kafin su koma garin su.
A irin wannan matsala akwai wacce ta mutu da ciwon zuciya da aman jini, don bayan ta rabu da iyayen ta ta biyo mijin ta shi da dangin su su ka dinga wulaƙanta ta, ba abinci, ga tsangwama. Mijin ya yi tafiyar sa ya bar ta. Har bara ta na yi don ciyar da yaran ta. Daga ƙarshe rana ɗaya ta kama aman jini, kafin a je asibiti ta mutu.
Irin waɗannan labaran su na da yawa, na kuma san wasu ma sun san irin labaran nan. Babbar matsalar abin shi ne sauran ƙabilu da addinai su na kallon abin a matsayin wata ɗabi’a tamu mara kyau. Don haka ni na fi ganin mu daina amfani da musuluntar da su mu na wulaƙanta su. Tabbas, shi aure ya na da rai amma rabuwa cikin bin ƙa’idojin Allah shi ya fi. Sannan gara ka auri mace don soyayya in dai ka na son ta. Kar mu ci gaba da amfani da musuluntar da su mu na kuma wulaƙanta su mu na ɓata wa Musulunci suna. Tunda mun yarda auri-saki matsalar mu ce, mu bar ta a tsakanin mu.
Na san wasu da hukumar Hisba na matuƙar ƙoƙari a kan irin wannan lamarin, amma ana karya zuciyar matan da yaran su. Mu yi ƙoƙarin zama jakadun addinin mu a kowace mu’amala, ba sai a sallah da azumi kawai ba.
Allah ya ganar da mu gaskiya, ya ba mu ikon bin ta, ya tsare mu da imanin mu amin.
* Fauziyya D. Sulaiman fitacciyar marubuciya ce kuma shugabar gidauniyar agaji ta Creative Helping Needy Foundation da ke Kano
![]()







