INNA lillahi wa inna ilahir raji’un! Allah ya yi wa mahaifiyar jarumin barkwanci Nasiru Auwal, wanda aka fi sani da Horo Ɗan Mama, rasuwa a yau.
Hajiya Ladi Auwal ta rasu ne da asubahin yau Asabar, 22 ga Agusta, 2020 da misalin ƙarfe 5:00.
Ta rasu a garin Gumel na Jihar Jigawa sanadiyyar ‘yar gajeruwar rashin lafiya na lokaci ɗaya.
Hajiya Ladi ta rasu ta na da kimanin shekaru 65 a duniya, kuma ta bar ‘ya’ya goma – maza 6, mata 4.
A lokacin da ya ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani kan wannan babban rashi, Nasiru ya fara ne da bayyana irin kusancin sa da ita, ya ce, “Allahu Akbar! Mama duk wani abu da za ta yi za ka ji ta ce Nasiru, duk motsin ta Nasiru!
“Ba ni kaɗai ba ne, (amma) wallahi ko bacci Mama ta ke yi ta na cewa Nasiru. Mun shaƙu sosai.
“Mama ko ɓata mata rai aka yi ina ƙoƙari in ga na faranta mata rai. Da na nuna mata ga-shi-ga-shi, nan take za ta yi fara’a, ta yi dariya, ta ji daɗi.”
Jarumin ya bayyana yadda aka yi zaton lokaci ya yi wa mahaifin sa, wanda ba shi da lafiya, amma ashe mutuwar na kan Hajiya ne. Ya ce: “Jiya warhaka ina tare da ita, mu na dariya da ita. Ta dafa abinci an kai wa mahaifi na, saboda na zo wurin mahaifi na ne ba shi da lafiya ya na asibiti. Abu na Allah, ita da kan ta ta fitar da rai da mahaifin mu, har ta ke ce mani, ‘Nasiru, sai dai a yi haƙuri da baban ku.’ Ashe Allah ba a nan lamarin sa ya ke ba!”
Haka kuma Nasiru ya faɗi yadda mahaifiyar tasa ta yi rasuwar bazata a motar sa, a daidai lokacin da ya kai ta asibiti. A cewar sa, “Wallahi yau da asuba ta ce a taso ni, na ɗauko mota, ta ce in kai ta asibiti. Na yi fakin, kafin mu fito da ita daga mota Allah ya ɗauki abin sa! Haka abin ya faru.”
A kan batun ko ‘ya’ya nawa ta bari, ya ce, “Mu dai a wurin mahaifiyar mu uwa ɗaya, uba ɗaya mu ke. Kuma mahaifiyar mu ita kaɗai ce a wurin mahaifin mu.”
A yayin da bada labarin rasuwar a shafin sa na Instagram ɗazu, Nasiru Horo Ɗan Mama ya rubuta cikin alhini cewa: “Inna lillahi inalillahi! al’umar Annabi ku taya ni da addu’a, mama na lokaci ya yi. Allah ya jiƙan ta da rahama. Allah ya sa Annabi ya karɓi baƙuncin ta.”
Allahu Akbar! To Allah ya jiƙan Hajiya da rahama, ya albarkaci dukkan abin da ta bari, amin.