A RANAR Talata mai zuwa, 24 ga Nuwamba, 2020 za a fara wani gagarumin taro kan yadda ake gudanar da bincike da rubuta labaran finafinai cikin harsunan Afrika. Taron, mai suna ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), za a gudanar da shi ne tsawon kwana biyu a Kano.
Alhaji Abdulkareem Muhammad, fitaccen ɗan jarida kuma ƙwararren mai shirya finafinai wanda tare da shi aka kafa masana’antar Kannywood, shi ne jigon shirya wannan bikin, wanda kamfanin sa, Moving Image, ya ke gabatarwa a duk shekara.
Wannan dai shi ne taro na uku, kuma a wannan shekarar an canza masa tsari, domin kuwa za a yi shi ne ta hanyar yanar gizo, wato salon nan na ga-ni-ga-ka da ake yi da manhajar Zoom.
A wannan tattaunawar da mujallar Fim ta yi da Alhaji Abdulkareem Muhammad, ya bayyana yadda taron zai kasance, da manufar sa, da kuma ƙalubalen da su ke fuskanta. Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen shi ne yadda kaf a masana’antar Kannywood babu ko da mutum ɗaya da ya yi rajista don shiga taron, bayan kuwa harshen Hausa ne zai karɓi baƙuncin taron finafinan da aka yi da wasu harsunan da ke nahiyar Afrika.
Ga yadda tattaunawar Alhaji Abdulkareem da wakilin mujallar Fim, MUHAMMAD LAWAN RANO, ta kasance:
FIM: Mecece manufar shirya wannan taro?
ABDULKAREEM MUHAMMAD: Wannan wani biki ne inda ake kambama finafinai na harshen Afrika baki ɗaya inda mu ke jawo hankalin mutane da su shigar da finafinan su da su ka yi da harsunan Afrika a cikin gasa domin mu fitar da zakarun da su ka yi fice a cikin wannan shirin. Kuma mu kan yi amfani da wannan dandalin mu horas da mutane a kan harkar yin fim. Sannan mu na yin taro da masana harkar yin fim ɗin su zo su gabatar da maƙaloli inda za a yi tambayoyi, sannan sai a wallafa littafi a kan waɗannan maƙaloli da aka gabatar.
FIM: Menene ya ja hankalin kamfanin ka ya shirya gabatar da taron ta yanar gizo?
ABDULKAREEM: Tun bayan da duniya ta fuskanci ƙalubalen cutar korona wanda kuma ya haddasa rashin walwala ga mutane wajen yin taro, to tunda wannan biki da mu ke yi na masu shirya waɗannan finafinan Afrika kuma a harsunan Afrika ba zai iya yiwuwa ba, shi ne sai mu ka ga bari mu ɗauko ɗaya daga cikin abubuwan da mu ke gabatarwa a cikin wannan biki, wato shirya taro da mu ke yi, inda ake kiran masana su gabatar da takardu ko ƙasidu a kan wani jigo da aka zaɓa. To sai mu ka ga cewa wannan dama ce, maimakon a ce wannan shekarar ba za a yi ba, gara a yi wannan taro.
Amma fa ba tara mutane za a yi ba, za a yi shi ne ta kafar ga-ni-ga-ka.
FIM: Zuwa yanzu ya ku ke ganin karɓuwar wannan taron a wajen al’umma?
ABDULKAREEM: Alhamdu lillahi, zuwa yanzu mun samu takardu ko kuma mutane waɗanda su ka nuna sha’awar cewa za su gabatar da takardu, bayan kuma mun samu mu ka tantance.
Kuma ina so in jawo hankali cewa wannan taro shi ne karo na uku; mun yi a 2018, 2019, wannan kuma shi ne na 2020. A karo na biyu da mu ka yi mun fara gwada wa al’umma irin abin da mu ke so mu yi, wannan kuma karo na uku da mu ka ce za mu yi wannan taro sai mu ka jawo hankalin Jami’ar Bayero, kuma da man su na da tsangayar koyar da aikin jarida, sai mu ka yi haɗin gwiwa da su kuma su ka shigo ka’in da na’in mu ke yin wannaan haɗin gwiwa.
Sannan kuma mun samar da kwamiti wanda ya ke shirye-shiryen wannan taro da za mu yi, sun kuma samo takardu da dama wanda ni ba zan iya cewa ga adadin su ba, amma dai daga ƙarshe an tantance kuma an amince da takardu guda ashirin da tara. Saboda haka daga yanzu a cikin kwana biyu ɗin nan takardun da za a gabatar sun kai har ashirin da tara.
FIM: Wane irin ƙoƙari ku ka yi don ganin kun wayar wa da jama’a kai kan wannan sabon tsarin da ku ka fito da shi?
ABDULKAREEM: E, da yake taro ne wanda ya ke bin zamani, kafofin sadarwa wanda ake amfani da su da su mu ka yi amfani wajen faɗakar da mutane. Mutum ya na daga gidan shi a duk inda ya ke a duniya zai halarta. Mu na da waɗanda za su gabatar da takardu daga ƙasar Jamus, mu na da waɗanda za su gabatar daga fannoni da kuma wurarare daban-daban. So, duk wanda ya ke so zai iya shiga wannan taro.
Kuma mun tanadi cewa za mu iya ɗaukar mutane dubu da za su hau kan abin da mu ke son mu yi, saboda haka kowa daga inda ya ke zai shiga wannan taron. Sannan in mutum ya na da tambaya zai iya yi kuma a ba shi amsa tamkar mutum ya na gurin ne. Haka za a yi.

FIM: Zuwa yanzu waɗanne irin ƙalubale ku ka fuskanta?
ABDULKAREEM: Ina ganin ƙalubalen dai shi ne musamman daga waɗanda su ke shirin finafinan Hausa, inda yake na farko dai Kano ita ce gurin da ake gudanar da wannan taro, sannan kuma Kano ita ce cibiyar da ake gudanar da shirin Kannywood – wato finafinan da ake yi na Hausa – sannan ba ta karɓi wannan shirin ba yadda ya kamata. Saboda me? Saboda ko yanzu da za a gabatar da takardun nan akwai waɗanda su ke daga jami’o’i daban-daban kan finafinan Hausa sun zaɓa za su yi, amma su waɗanda su ke shirin su na finafinan Hausan ba wani guda ɗaya wanda zai gabatar da takarda a kan wannan da za mu yi, wanda kuma na ke ganin hakan ƙalubalen ba kaɗan ba ne, a ce harshen ka shi ne zai karɓi baƙuncin wasu finafinan da aka yi na wasu harsunan, amma kai ba ka tashi ka yi yunƙurin ka nuna kan ka ba a cikin dandamali ko kuma kafa. Ina ganin wannan ƙalubale na farko kenan.
Ƙalubale na biyu kuma, hatta ita gwamnati abin da wannan abin zai jawo mata ba kaɗan ba ne, na cewa a ce ana taro na nahiyar Afrika baki ɗaya amma a ce gwamnati ba ta shigo cikin harkar ta yi dumu-dumu ta ga yadda za ta yi ta taimaka ba. Shi ma wani ƙalubale ne babba.
Sannan wato idan mu ka duba yanayi na cewa yanda za a yi wannan gabatar da taron, har yanzu ƙasar mu ba ta kai a ce ta na da kafar da za a buɗo nata ba a yi irin wannan taron, na wasu ne mu ka yi. Saboda haka ka ga mu na miƙa kan mu da yadda komai mu ke yi ba mu da sirri, wasu ne su ke riƙe da bayanai a kan mu. To wannan ina ganin shi ma ƙalubale ne wanda ya kamata a ce a gwamnatance kamar hukumar NCC da mu ke da ita, wato Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, ya kamata a ce su ne waɗanda su ke ba mu kafar yadda za mu iya aiwatar da irin wannan taron, sannan kuma sai wanda su ka tantance zai iya samun bayanai a kan abin da mu ke yi, saboda ƙasa in ta na so ta ci gaba dole irin waɗannan abubuwan sai ta sa ido a ciki.

FIM: Ba ka ganin rashin wayar wa ‘yan Kannywood da kai a kan abin shi ya sa ba su shiga ba?
ABDULKAREEM: Wato shi Bahaushe ya na da shagala; ko meye na Malam Bahaushe ya na mai riƙon sakainar kashi, hatta ran shi. In ka duba yadda za ka tsallaka titi, yanda za ka yi abu ba tare da ka na la’akari da wani abu da zai kare mutuncin ka ko kishin wani abu na al’ada da tarbiyya saboda Bahaushe bai riƙe al’adar shi da tarbiyyar shi yadda ya kamata ba. Saboda haka ba abu ne na masu harkar fim ba, abu ne namu na Hausawa. Saboda haka, halin Bahaushe ne ya ke shafar mu. Ko da an yi wani abu da za a faɗakar da kai, ka riga ka ɗau wani matsayin ka wanda kuma ba za a iya faɗakar da kai ɗin nan ba.
To amma ala kulli halin, komai na rayuwa ba a yin sa da garaje kuma ba a ƙarfafa shi da gaggawa. Saboda sanin haka, mu mu na nan mu na bada lokaci da cewa waɗanda ya kamata su fahimta ɗin Allah zai nufe su da su fahimci abin da ake nufi har su hau kan turbar.
FIM: Menene kiran ka ga jama’a a matsayin ku na waɗanda su ka ga jiya kuma su ke ganin yau a wannan fannin na shirya finafinai?
ABDULKAREEM: Kira na ga al’umma shi ne wato ita harka ta fim, harka ce da wani masani ya ce duk wanda ya ke cikin wannan harkar kamar mai buɗe ƙwaƙwalwar ɗan’adam ne. Idan mutum zai auna ƙwaƙwalwar ka, to ba ƙaramin muhimmanci za ka ba shi ba. Saboda me? Saboda ba wai kai ƙwaƙwalwar ka a matsayin mutum ɗaya ka ke yi ba, a’a, a matsayin al’umma. Shirin da ake yi ya na shiga ƙwaƙwalwar yaran mu, ya na shiga ƙwaƙwalwar matan mu, ya na shiga ƙwaƙwalwar al’ummar mu. To amma har yanzu ba mu fahimci cewa ya kamata mu shigo wannan harka mu tsaftace ta yadda za ta kiyaye al’ummar mu ba. Ni ina ganin wannan shi ne babban kiran da zan yi ga fahimtar da ake wa harkar fim.
Ya kuma kamata mu san cewa ba za mu iya tsayar da ita ba, abin da ya kamata mu yi shi ne mu canza ta, lafazin ta da yanayin ta ya kasance ya na wakiltar mu. Amma ba wai mutum ya tsaya ya kushe abu da baki ba, aljihun shi kuma a tsuke, sannan ilimin sa ya killace wa kan shi. To ba ƙaramin rashin adalci mu ke wa kan mu ba in mun bi ta wannan matsayin.
FIM: Idan jama’a su na da sha’awa ko son shiga wannan taron, ya zai yi ya same ku?
ABDULKAREEM: Akwai shafin mu na yanar gizo, wato https://kilaf.movingimage.africa, idan mutum ya shiga nan za ta buɗe mashi wurin da zai shiga ya yi rajista, kuma in ɗalibi ne zai nuna shaidar shi ta ɗalibi, sannan kuma ba zai biya ko kwabo ba. Amma wanda ya ke ba ɗalibi ba in ya shiga za ta buƙaci ya zaɓi kafofi ko da uku wanda zai iya biya. Kuma kuɗin N2,500 ne. Idan mutum ya yi wannan rajista ɗin za a ba shi yadda zai kama mu ta yanar gizo ɗin nan a lokacin da ake yin taron.
![]()






