• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista ta ƙaddamar da shirin tallafa wa matan karkara da jari a gabashin Nijeriya

by DAGA WAKILIN MU
November 20, 2020
in Nijeriya
0
Matan gabashin Nijeriya a wajen taro

Matan gabashin Nijeriya a wajen taro

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SHIRIN nan na Gwamnatin Tarayya na raba agajin tsabar kuɗi ga matan karkara, wato ‘Cash Grant for Rural Women’, yanzu ya fara aiki a yankin kudu-maso-gabashin ƙasar nan.
 
Hakan ya biyo bayan ƙaddamar da shirin wanda Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi a Jihar Ebonyi a ranar Alhamis da ta gabata.  
 
A wajen taron ƙaddamarwar wanda aka yi a tsohon Gidan Gwamnati da ke garin Abakaliki, ministar ta shawarci matan da aka raba wa kuɗin da su kashe wannan biya sau ɗaya na N20,000 ga kowaccen su ta hanya mai kyau, musamman wajen ƙara jarin ƙananan sana’o’in da su ke da su.
 
Ta bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ce ta kafa shirin don ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa a cikin shekaru goma.
 
Ta ce: “Saƙon mu a gare su shi ne su yi amfani da wannan kuɗi ta hanya mai kyau wajen fara ƙananan sana’o’i  ta yadda cikin yardar Allah wannan kuɗi zai ruɓanya yawan sa har su samu damar kula da kan su da iyalan su.
 
“Mu na fatan gwamnatin Jihar Ebonyi za ta taimaki waɗannan matan da shawarwari tare da  goyon baya da sanin makamar aiki, ta ci gaba da ɗora su a kan hanyar gudanar da sana’ar da kowace mace ta zaɓa.”
 
Cikin nasa jawabin, Gwamnan Jihar Ebonyi, Injiniya David Umahi, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda wannan shirin wanda ya ce zai taimaka gaya wajen rage wahalhalun da matan karkara su ke ciki a jihar.
 
Gwamna Umahi, wanda Mataimakin Gwamna Eric Kelechi Igwe ya wakilta a taron, ya bayyana ziyarar da ministar ta kai da cewa ta zo a kan kari, sannan ya yi alƙawarin cewa matan za su fara cin moriyar kuɗin jarin da aka ba su nan ba da jimawa ba.
 
Ya ce, “Wannan babbar rana ce domin rana ce kuma da mutanen Ebonyi su ka tashi daga ɓangaren hagu zuwa na dama. Babu wata gwamnati da ta taɓa yi wa mutanen Ebonyi irin wannan. 
 
“Na gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da Minista Sadiya Umar Farouq saboda fito da waɗannan tsare-tsare na cigaban ƙasa.
 
“Mata mutane ne masu himma. In da maza ne su ka samu wannan kuɗin, washegari sai ka ji za su yi aure da kuɗin. 
 
“Mata ba su ba maza umarni, to amma su kan tabbatar da cewa akwai abinci a gida. Saboda wannan abin alheri,  mu na godiya, kuma za mu ci gaba da kawo ƙoƙon barar mu.”
 
Haka kuma mataimakin gwamnan ya yi kira ga ministar da ta fito da hanyoyin da za a riƙa sa ido kan shirin don auna yadda matan ke ci gaba da amfana da shi a kasuwancin su ko kuma duk abin da su ka yi da kuɗin jarin.
 
Ana sa ran sama da mata 200 daga ƙananan hukumomi 13 da ke Jihar Ebonyi ne za su amfana daga wannan shiri na Gwamnatin Tarayya mai suna ‘Cash Grant for Rural Women’.

Loading

Previous Post

Shirin tallafa wa matan karkara da kuɗi ya na ceton rai – Ladan Salihu

Next Post

Abdulkareem: Yadda taron finafinan Afrika na ‘KILAF 2020’ zai kasance

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Alhaji Abdulkareem Muhammad a cikin 2018

Abdulkareem: Yadda taron finafinan Afrika na 'KILAF 2020' zai kasance

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!