• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shirin tallafa wa matan karkara da kuɗi ya na ceton rai – Ladan Salihu

by DAGA WAKILIN MU
November 18, 2020
in Nijeriya
0
Ministar Harkokin Jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, tare da Ministar Harkokin Mata, Dame Pauline Tallen, lokacin raba kuɗin tallafi a Bauchi da Gombe

Ministar Harkokin Jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, tare da Ministar Harkokin Mata, Dame Pauline Tallen, lokacin raba kuɗin tallafi a Bauchi da Gombe

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Shugaban Ma’aikata a ofishin Gwamnan Jihar Bauchi, Dakta Ladan Salihu, ya bayyana shirin nan na tallafin matan karkara da kuɗi, wato ‘Rural Women’s Cash Transfer Programme’, da cewar shiri ne na ceton rai a jihar. 

Dakta Salihu ya faɗi haka ne cikin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce dukkan matan da su ka amfana daga shirin sun samu sana’ar yi ta hanyar tattalin jarin da su ka samu daga shirin. 

 Ya ce: “Na yi amanna da cewa wannan shiri zai cimma manufofin da aka kafa shi domin su idan aka yi la’akari da irin masu cin moriyar sa a Jihar Bauchi. 

 “Bari in faɗa maku abin da na fahimta game da wannan shiri. Lokacin da na ke wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan bincike kafin mai girma Minista ta iso, akwai mata sama da 1,200 da su ke jira a waje. Na ga wasu matan kimanin guda 50 waɗanda tun farko ba su yi rajista da shirin ba ko ba a ɗau sunan su ba. Sai na ce kawai a ba su dama su shigo ciki. 

 “Wasu daga cikin matan guragu ne, da sauran nau’o’i na naƙasa.  

“Abin da ya ba ni mamaki da sha’awa shi ne lokacin da na shigo, yawan matan da na gani  a ciki su ne a waje. Duk sai aka shigar da su, aka ɗau sunayen su, yanzu sun shiga cikin  masu cin moriyar shirin.

Mata a wurin taron karɓar tallafin kuɗi a Bauchi

“Ina so in taya Mai Girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari murna kuma in yi jinjina ga mai girma Minista Sadiya Umar Farouq saboda wannan muhimmin shiri na  ceton rayuwa wanda ya ke gyara rayuwa tare da inganta ta.”

 A kan batun kayan aiki da hanyoyin raba tsabar kuɗin a Jihar Bauchi, Dakta Salihu wanda a da shi ne Darakta-Janar na Hukumar Rediyon Tarayya ta Nijeriya, ya bayyana gamsuwa kan hanyoyin da ake bi ana zaɓar matan da ke amfana da shirin. 

Ya ce: “Na gamsu matuƙa da irin shirye-shiryen da aka yi, da kayan aikin da dukkan tsarin da ake bi da yadda aka gudanar da aikin cikin tsanaki ba tare da wani cikas ba.

 “Tare da ni aka yi aikin rabon kuma ina tabbatar maku cewa, daga abin da na gani, na gamsu babu wata tantama cewa manufofin wannan shiri ana tsara su ne a tsanake kuma a aiwatar da su ta ingantacciyar hanya.” 

Sama da mata 4,000 a ƙananan hukumomi 20 da ke Jihar Bauchi ne kowacce za ta karɓi N20,000 a ƙarƙashin wannan shiri wanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta shirya domin ceto marasa ƙarfi daga ƙangin talauci.

 Zuwa yanzu, sama da mutum 78,000 ne su ka amfana daga tsare-tsaren rage ƙuncin rayuwa a Jihar Bauchi.

Loading

Previous Post

Mai ƙarar Rahama Sadau ya haƙura

Next Post

Minista ta ƙaddamar da shirin tallafa wa matan karkara da jari a gabashin Nijeriya

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Matan gabashin Nijeriya a wajen taro

Minista ta ƙaddamar da shirin tallafa wa matan karkara da jari a gabashin Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!