• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, August 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mu guji duk abin da zai jawo farraƙa tsakanin Hausawa da Fulani – Aminu Ala

by MUKHTAR YAKUBU
August 12, 2026
in Al'adu
0
Mu guji duk abin da zai jawo farraƙa tsakanin Hausawa da Fulani – Aminu Ala

Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) yana karɓar karramawar da ƙungiyar raya al’adu da masarautun gargajiya mai suna Royal Tridiagonal Centre (RTC) ta yi masa a babban taron da ta yi a Kano a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHAHARARREN mawaƙin nan, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya yi kira ga al’umma da su guji duk wani abu da zai haifar da saɓani ko rashin jituwa tsakanin Hausawa da Fulani, yana mai cewa ya kamata a ƙarfafa abubuwan da suka haɗa al’ummomin biyu maimakon mayar da hankali kan abubuwan da za su raba su.

Ala ya faɗi hakan ne a wajen wani babban taro na ƙasa wanda Ƙungiyar Raya al’adu da Masarautun Gargajiya, wato Royal Tridiagonal Centre (RTC), ta gudanar da nufin farfaɗo da kyautata alaƙa tsakanin al’ummar Arewa, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar ƙoƙarin haifar da gaba da ƙiyayya tsakanin Hausawa da Fulani.

Taron, wanda aka gudanar a Ɗakin Taro na Rabi’u Musa Kwankwaso da ke Kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano.a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, ya mayar da hankali ne kan raya al’adu, kare martabar masarautun gargajiya da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma.

Ƙungiyar ta kuma karrama wasu fitattun mutane da ta ce suna bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya da cigaban al’ummar Hausawa da Arewa baki ɗaya.

Daga cikin fitattun mutanen da aka karrama akwai shahararren mawaƙin nan, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa).

Da yake jawabi bayan karɓar karramawar, Ala ya bayyana farin ciki da godiya ga ƙungiyar bisa zaɓar sa cikin mutanen da ta ga sun cancanci a karrama su saboda gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.

Mawaƙin ya yi kira ga al’umma da su guji duk wani abu da zai haifar da saɓani ko rashin jituwa tsakanin Hausawa da Fulani, yana mai cewa ya kamata a ƙarfafa abubuwan da suka haɗa al’ummomin biyu maimakon mayar da hankali kan abubuwan da za su raba su.

Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) jim kaɗan bayan ya karɓi karramawar da aka yi masa

A cewar sa, a halin yanzu Hausawa da Fulani sun kasance al’umma mai kusanci sosai, sakamakon abubuwan da suke da alaƙa da su, ciki har da zama a wuri guda, addini guda da kuma auratayya tsakanin juna.

Ya ƙara jaddada cewa haɗin kai da zaman lafiya su ne ginshiƙan cigaban al’umma, don haka ya kamata shugabanni da masu ruwa da tsaki, da kuma ɗaiɗaikun mutane, su taka rawar gani wajen hana duk wani yunƙuri na raba kan Hausawa da Fulani.

Ala ya ce karramawar ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da amfani da fasahar sa da matsayin sa a cikin al’umma wajen isar da saƙonnin zaman lafiya, haɗin kai da kuma kare al’adun Hausawa.

Loading

Tags: al'aduAminu Alan WakaFulaniHausawakarramawaƙungiyamasarautu
Previous Post

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

Related Posts

Gwamna Abba Kabir Yusuf yana Jawabi a wajen taron
Al'adu

Ranar Al’adu ta Duniya: Gwamnan Kano na so a yi riƙo da al’adun gargajiya

August 10, 2025
Al'adu

Kare Sabbin Kalmomin Hausa “Saskiyā” (Synonym) da “Gīɗiyā” (Antonym) ta Hanyar ‘Yancin Binciken Ilimi

May 22, 2025
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kadara ne mai daraja ga Jihar Kano
Al'adu

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kadara ne mai daraja ga Jihar Kano

January 28, 2024
Minista Hannatu Musawa ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tarihi da Gidan Wasanni na Ƙasa a Abuja
Al'adu

Minista Hannatu Musawa ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tarihi da Gidan Wasanni na Ƙasa a Abuja

December 14, 2023
Khalifa Muhammadu Sanusi II
Al'adu

Sanusi: Magajin Sanusi da Kukuna

June 23, 2023
Shugabannin ƙasashen Afrika a wajen wani babban taron su a Habasha
Al'adu

Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta zaɓi Swahili a matsayin harshen da za ta riƙa aiki da shi

February 10, 2022
  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!