INNA lillahi wa inna ilaihi raji’un! A llah ya yi wa wani tsohon ɗan wasan Hausa mai suna Ibrahim Mu’azzam rasuwa a Kano.
Mujallar Fim ba ta samu cikakken bayani game da jarumin da rasuwar tasa ba, amma an ce ya fito a wasu finafinai a shekarun baya.
Alhaji Auwal Muhammad Sabo, furodusa kuma shugaban kamfanin Sarauniya Films, Kano, ya tura sanarwa a Facebook ɗazu inda ya ce: “Allahu Akbar! Ubangiji Ya karɓi ran Ibrahim Mu’azzam jiya da dare. Ɗazu aka yi jana’izar sa.
“Ibrahim ya ɗan fito kaɗan a wasannin Hausa shekarun baya.
“Ya fito a abokin Ibrahim Mandawari a fim ɗin ‘Garwashi’.”
Ganin wannan saƙo, ɗimbin mutane sun yi ta’aziyyar rasuwar wannan bawan Allah, cikin su har da ‘yan fim.
Mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya yafe masa kurakuran sa, ya saka masa da gidan Aljannar Firdausi, amin.