• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar mahaifiyar Sarkin Kano rashi ne gare mu, inji ‘yan Kannywood

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
April 29, 2021
in Labarai
0
Rasuwar mahaifiyar Sarkin Kano rashi ne gare mu, inji ‘yan Kannywood
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GAMAYYAR ƙungiyoyin masu shirya finafinan Hausa sun bi sahun al’ummar Nijeriya wajen taya Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, alhini bisa rasuwar mahaifiyar sa, wato Mai Babban Ɗaki, Hajiya Maryam Ado Bayero.

Marigayiyar, wadda matar tsohon Sarkin Kano Ado Bayero ce kuma uwa ga Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero, ta rasu ne a wani asibiti a ƙasar Masar a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, 2021.  

‘Yar shekara 80 a duniya, an yi jana’izar ta a ranar Litinin, 26 ga Afrilu a Ƙofar Kudu, wato gidan Mai Martaba Sarki.

A yayin da ɗimbin jama’a daga sassa daban-daban ke ci gaba da zuwa ta’aziyya ga Mai Martaba Sarki, su ma ‘yan fim ba a bar su a baya ba.

A yau Alhamis, 29 ga Afrilu, wasu daga cikin jagororin ƙungiyoyin Kannywood sun kai wa Sarki ziyarar ta’aziyya a madadin sauran ‘yan fim bisa wannan babban rashi da aka yi.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya na karɓar gaisuwa daga shugabannin ‘yan fim

Waɗanda su ka jagoranci ziyarar sun haɗa da shugaban riƙo na MOPPAN da shugaban Gidauniyar Kannywood (wato Kannywood Foundation) da kuma wasu daga Zauren Dattawan Kannywood (wato Kannywood Elders Forum). 

Da ya ke jawabi, shugaban Zauren Dattawan Kannywood, Malam Auwalu Isma’il Marshal, ya bayyana mutuwar Mai Babban Daki a matsayin babban rashi da aka yi wa Jihar Kano baki ɗaya, ba wai ga Mai Martaba Sarki kaɗai ba.

Marshal ya ce, “Ita Mai Babban Ɗaki uwa ce gaba ɗaya a gare mu. Saboda haka mun zo mu yi ta’aziyya da kuma jajantawa, da fatan Allah ya yi mata rahama. Shi kuma Mai Martaba Sarki Allah ya ba shi haƙurin jure wannan rashi.”

Shi ma a nasa jawabin, shugaban MOPPAN reshen Jihar Kano, Salisu Muhammad (Officer) ya ce, “Wannan ta’aziyya  da ma ya kamata a ce tun da fari mun gayyato mutanen mu mu zo a yi ta, saboda irin dangantaka mai ƙarfin gaske da ta ke a tsakanin wannan masana’anta da kuma masarautar Kano  tun kafin ya zama Sarkin Kano.

“Ba wanda mu ke alfahari da shi a cikin wannan masana’anta kamar shi. Kamar yadda mu na gayyatar sa abubuwan mu ya zo, mu ma kuma ya na gayyatar mu. Don haka wannan rashi ne ga dukkannin masana’antar shirya finafinai ta Hausa.

“Mutumin mu ne, kuma ya ba mu gudunmawa mai yawa a cikin wannan sana’a tamu.”

A lokacin ziyarar ta’aziyyar, mujallar Fim ta ga manyan ‘yan fim da su ka haɗa da Auwalu Marshal, Shu’aibu Yawale, Salisu Officer, Kabiru Maikaba, Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, Ɗan’azumi Baba (Kamaye), Bashir Bala Ciroki, Bala Anas Babinlata, Mustapha Musty da Nura Mado.

Mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya yi mata rahama, ya ba iyalan masarautar ikon jure wannan babban rashi.

Daga hagu: Nura Mado, Auwalu I. Marshal, Hamisu Iyan-Tama, Bala Anas, Shu’aibu Yawale, Mustapha Musty, da Salisu Officer … a gidan Sarkin Kano

Loading

Previous Post

Za a yi Babban Zaɓen 2023 a ranar 18 ga Fabrairu – INEC

Next Post

Tsohon jarumi Ibrahim Mu’azzam ya kwanta dama

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Tsohon jarumi Ibrahim Mu’azzam ya kwanta dama

Tsohon jarumi Ibrahim Mu'azzam ya kwanta dama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!