SHAMSUDDEEN Surajo ya daɗe ya na gaganiyar yadda zai samu hanyar dogaro da kai, maimakon zaman jiran aikin da bai san ranar samu ba. Faɗi nan, tashi can, har Allah ya sa ya yi gamo-da-katar ɗin samun aikin N-Power. Ɗan alawus ɗin da ya riƙa samu bai almubazzarantar da su ba. Sai ya riƙa tara ƙudin sa a banki.
Bayan wa’adin aikin sa ya ƙare, Shamsuddeen ya nemi ƙarin gudunmawa wajen abokan sa, inda ya buɗe shagon ɗinki a Hausawa, Kano.
“Wato a baya idan Sallah ta zo ko ɗinki ba na iya yi wa kai na. Amma a yau ni ne har layi masu kawo ɗinki ke yi a shago na. Ka ga kuwa wannan rufin asirin fa sanadiyyar N-Power ne.
“Shi ya sa a yanzu da aka buɗe ‘Batch C’, na riƙa nuna wa matasa muhimmancin aikin N-Power,” inji shi.
Irin yadda Shamsuddeen ke yabo da godiya ga shirin N-Power, haka za ka ji duk inda matasa su ke a faɗin ƙasar nan babu wani zance a bakin su mafi ma’ana ko muhimmanci ga inganta rayuwar su kamar N-Power. A yanzu ko hirar ƙwallon ƙafa ba ta kai N-Power shiga zukatan matasa ba.
Shirin N-Power ya na ɗaya daga cikin tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da shi, kuma ya ke ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa. A yanzu wannan shiri ya na a sahun gaba da gwamnatin Muhammadu Buhari ke tinƙaho da shi a sahun tsare-tsaren ta na fitar da mutum miliyan 100 daga ƙangin talauci nan da shekara goma, wanda wannan gwamnati ta ƙudiri aniyar tabbatarwa.

Akwai albarka mai ɗimbin yawa a shirin. Baya ga inganta rayuwar marasa galihu, shirin ya na zaburar da masu cin moriyar sa su koyi dabarun tattalin tara kuɗaɗen kama sana’ar dogaro da kai. N-Power rufin asirin iyali ne, domin idan mutum miliyan ɗaya su ka amfana, kowane zai iya ciyar da yara uku. Wato tamkar an inganta rayuwar mutum miliyan huɗu kenan.
Duk wanda ya amfana da N-Power daga nan ya ke miƙewa hanyar dogaro da kai. Isma’il Abubakar kuwa cewa ya yi, “Ka gan ni nan, suna na har ɓacewa ya yi saboda ina yawan kiran N-Power. Sai ake ce min ‘N-Power’ saboda shirin ya maida ni mutum. Na amfana kuma na san waɗanda su ka amfana da shirin masu yawan gaske.”
‘Shirin N-Power Na Batch C’: Gabatowar Inganta Rayuwar Matasa Miliyan Ɗaya
A ranar 11 ga Maris, 2021 aka buɗe rumbun shiga a cika fom na N-Power ‘Batch C’ a ƙarƙashin Shirin Inganta Rayuwar Jama’a (NASIMS). Tun a ranar da aka buɗe aka sanar da cewa a zabura a cika fom a intanet kuma a shirya yin gwaji na dole kan duk wanda ya shiga ya cika fom ɗin.
Yayin da aka shiga watan Mayu har sama da mutum miliyan 1.8 sun cika fom. Sai dai kuma bayan an tantance, an zaƙulo sunayen mutane 550,000, waɗanda a cikin su ne za a rauraye, a ɗauki mutum 500,000 aikin N-Power a rukunin farko na ‘Batch C’. Daga nan kuma ɗaukar mutum 500,000 zai sake biyo baya, a matsayin cikon mutum miliyan ɗayan da ke ƙarƙashin ‘Batch C’ kenan.
Saboda haka ne Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta bada sanarwar cewa waɗanda su ka cike fom su riƙa tuntuɓar lambobin waya 08188883416 ko 081 76551162 domin neman ƙarin bayani, ko kuma i-mel: support npower@nasims.gov.ng.
Kawaji ya rubuto ne daga Kano
