• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mutuwar tsohon jarumin Indiya, Dilip Kumar, ta girgiza Bollywood

by DAGA IRO MAMMAN
July 7, 2021
in Labarai
0
Mutuwar tsohon jarumin Indiya, Dilip Kumar, ta girgiza Bollywood
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MASANA’ANTAR finafinan Indiya, Bollywood, ta kaɗu sosai sakamakon rasuwar ɗaya daga cikin manya kuma tsofaffin jarumai Dilip Kumar a yau Laraba, 7 ga Yuli, 2021.

Kumar ya na daga cikin jaruman da ake matuƙar girmamawa a Bollywood.

Ya rasu ya na da shekara 98 a duniya.

Saƙonnin ta’aziyya cike da alhini su na ci gaba da kwararowa daga sassa daban-daban na masana’antun shirya finafinai na ƙasashen Indiya da Pakistan.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa sunan yanka na Kumar dai shi ne Mohammed Yusuf Khan, kuma an haife shi ne a ranar 11 ga Disamba, 1922, a garin Peshawar na Pakistan, a lokacin da ƙasar ta ke haɗe da Indiya a ƙarƙashin mulkin mallaka na Birtaniya. Mahaifin sa mai sayar da kayan narmari irin na lambu ne; shi ne ya ɗauke iyalin sa zuwa birnin Mumbai inda nan ne cibiyar sana’o’in nishaɗantarwa ta Indiya, a shekarun 1930.

Ɗaya daga cikin manya-manyan rol na Dilip Kumar da aka fi tunowa da su shi ne fitar sa a fim ɗin soyayya ta tarihi ɗin nan mai suna ‘Mughal-e-Azam’, wanda aka yi a kan wani babban ɗan sarkin Mughal. Ya kasance ɗaya daga cikin finafinan Indiya da su ka wazgo riba a tarihi.

Kumar, wanda ya ambaci manyan jaruman Hollywood ɗin nan Marlon Brando da Gary Cooper da kuma Spencer Tracy a matsayin waɗanda su ka yi tasiri a rayuwar sa ta industiri, ya yi fice daga bisani a cikin 1964 saboda fitowar sa a fim ɗin kishin ƙasa ɗin nan mai suna ‘Leader’, wanda aka shirya kan yaƙe-yaƙen da Indiya ta yi a kan Chaina da Pakistan.

Kumar ya auri jaruma Saira Banu a cikin 1966, lokacin ya girme ta da shekara 22.

Jim kaɗan da ɓullar labarin rasuwar, ɗimbin masu ruwa da tsaki a Bollywood sun garzaya gidan marigayin domin yin ta’aziyya.

Shah Rukh Khan, Ranbir Kapoor, Karan Johar, Johnny Lever, Vidya Balan-Siddharth Roy Kapur, da Anupam Kher, su na daga cikin manyan ‘yan Bollywood da su ka garzaya gidan. An ga jarumi Shah Rukh Khan ya na zubar da hawaye lokacin da ya ke faɗa wa Saira Banu ta ɗau haƙuri a kan mutuwar mijin ta.

Su ma ‘yan siyasa ba a bar su a baya ba wajen miƙa saƙon ta’aziyyar su. Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi, ya kira Kumar da “gwarzon sinima”. Ya ce a Twitter, “Allah ya albarkace shi da hikima. Mutuwar sa wata asara ce ga duniyar al’adun mu.”

Shi ma Firayim Ministan Pakistan, Imran Khan, ya shiga sahun masu aikawa da saƙonnin ta’aziyya a ranar Laraba, inda ya gode wa Kumar saboda taimakon da ya bayar wajen yekuwar neman agajin kuɗi saboda ƙananan yara masu fama da ciwon daji. Ya ce shi “ɗan wasa ne mafi girma kuma mafi gwaninta” a cikin tsararrakin sa.

Babban Ministan Jihar Maharashtra ta ƙasar Indiya, Uddhav Thackeray, da jagoran jam’iyyar NCP ta ƙasar, Sharad Pawar, su ma sun ziyarci gidan Dilip Kumar domin yin gaisuwa.

An shiga shirin gudanar da jana’izar Dilip Kumar a Mumbai a yau. ‘Yan sanda sun kulle layukan da ke kusa da gidan sa saboda gudun cincirindon ‘yan kallo.

Loading

Tags: BollywoodDilip KumarFinafinan IndiyaIndian actorsIndian films
Previous Post

Gwamnati ta soma sake nazarin Dokar Haƙƙin Mallaka

Next Post

Yadda shirin N-Power ke zaburar da miliyoyin matasa taka tudun dogaro da kai

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Yadda shirin N-Power ke zaburar da miliyoyin matasa  taka tudun dogaro da kai

Yadda shirin N-Power ke zaburar da miliyoyin matasa taka tudun dogaro da kai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!