MURNA ta lulluɓe masu harkar finafinan Hausa a daren yau sakamakon labarin da aka samu cewa ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako furodusan nan Alhaji Ali Bulala Gusau.
Idan kun tuna, mun ba ku labari a jiya cewa ɓarayi sun sace shi tare da iyalin sa a hanyar Gusau zuwa Sakkwato shekaranjiya.
Daga baya iyalin nasa su ka kuɓuta, shi kuma sai ɓatagarin su ka yi garkuwa da shi tare da sharaɗin sai an biya diyyar naira miliyan 30 kafin su sako shi.
To alhamdu lillahi, Ali dai ya dawo gida Gusau cikin iyalan shi.
Sai dai mujallar Fim ba ta samu bayani kan yadda aka yi har ya kuɓuta ba.
Wakilin mu ya ga hoton furodusan tare da wasu ‘yan’uwan sa, ya na riƙe da babbar riga shadda wadda ta cumuimuye.
Mu na fatan Allah ya bi masa haƙƙin sa, kuma ya kiyaye gaba, amin.