• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Martani: Abubuwan dubawa a cikin tsokacin Iyan-Tama

by DAGA TY SHABAN
September 26, 2021
in Tsokaci
0
TY Shaban

TY Shaban

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

NA karanta tsokacin da Alhaji Hamisu Iyan-Tama ya yi a mujallar Fim kan haramcin yin fim a kan kidinafin, shaye-shaye da ƙwacen waya kamar yadda Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta sanar. Sai dai ina da ɗan tsokaci da na ke son yi kan abubuwan da Iyan-Tama ya rubuta, kamar haka:

1. Ya nuna ilimin da ya ke da shi a cikin sana’ar fim. Wannan gaskiya ne duba da daɗewar sa a cikin sana’ar da matakan nasara da ya taka.

2. Ya bayyana ƙa’idoji da tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya. Amma na rasa ganin wata saɗara a cikin dokokin da ta haramta yin finafinai da ke ɗauke da abubuwan da ake magana a kan su.

3. Ya bayyana ƙarara yiwuwar daina fim idan buƙatar hakan ta taso. Amma bai zayyana tanade-tanaden da ya kamata a gan su a ƙasa ba ko ba wa gwamnati shawara a kan abin da ya kamata ta yi domin guje wa asara da rashin fahimta.

4. Ya bayyana rabe-rabe (classification) na fim da kowane rukunin mutane ya kamata su kalla. Amma na kasa gane menene laifin furodusoshi da su ke samar da kowane ‘classification’ na fim bisa doka. Ko ko haƙƙin furodusa ne saka hatimin tantance kowanne fim? Ko ko haƙƙin su ne bada izinin kallon fim a gidaje da wurin kallo?

Isma'il Afakallah (a hagu) da Hamisu Iyan-Tama
Isma’il Afakallah (a hagu) da Hamisu Iyan-Tama

5. Ya bayyana shiriya a wurin Allah ta ke, ya kuma nuna fim na dabanci bai ɓata irin su ba da sauran mutane. Amma ya gaza bada misali da wani fim na wannan zamani da ya ɓata mutane. Ko shiriyar ta Allah ta ƙare ne? 

6. Ya bayyana cewa Afakallah ya ɓata rawar sa da tsalle wurin ɓatawa da jama’a. Wataƙila Afakallah a kan doka da oda ya ke tafiya ko kuma su waɗannan mutane ma’abota karya doka ne. Cikin biyu dai a yi ɗaya!

7. Ya soki Afakallah wurin karya masa tattalin arziki da hana shi fitar da fim ɗin sa. Amma ya manta irin dokokin da ya zayyana a baya su ne su ka hana fitar da fim ɗin saboda ya saɓa wa dokokin tace finafinai na Jihar kano.

8. Ya bayyana rashin ba shi kuɗin gudanar da aikin kwamitin kasuwancin fim da ya jagoranta a matsayin rashin adalci. A nan, akwai alamar kawo kuka da ladabi wurin Hukumar Tace Finafinai domin samun makoma.

Kaɗan daga cikin tsokaci na kenan.

* TY Shaban fitaccen furodusa ne, mawaƙi kuma jarumi a Kannywood

Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: Censorship in Nigeriadokadrug abusegwamnatiHamisu Iyan-Tamahausa filmsHukumar Tace Finafinai ta Jihar KanoIsmail na'abba afakallahKannywoodKano State Censorship BoardkidinafinKidnappingmatasaNFVCBshaye-shayeta'addanciTY Shaban
Previous Post

Tsakanin gwamnatin Kano da ‘yan Kannywood

Next Post

Bayan wata 10, Mustapha Musty da Soha sun samu ɗan fari

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Samɓalelen ɗan da Soha ta haifa wa Musty a yau. Allah ya raya!

Bayan wata 10, Mustapha Musty da Soha sun samu ɗan fari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!