AN yi wa babban ɗan Sarkin Kano, Kabiru Bayero, baiko da ɗiyar shahararren attajirin nan kuma ɗan siyasa da ke Sakkwato, Alhaji Ummarun Kwabo AA, baiko.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Kabiru, wanda ya yi digirin sa a fannin Harkar Kasuwanci, zai auri yarinyar mai suna A’isha Ummarun Kwabo nan ba da daɗewa ba.
A rahoton, wanda mujallar Fim ta gani, an bayyana cewa wata babbar tawaga da ta tashi daga masarautun Kano da Bichi ta je Sakkwato jiya Asabar domin nema wa ɗan sarkin auren.
Tawagar, wadda Wazirin Kano, Alhaji Sa’ad Giɗaɗo, ya jagoranta, ta ƙunshi Sarkin Dawaki Maituta na Kano, Alhaji Abubakar Bello Tuta; Ɗan’isan Kano, Alhaji Kabiru Tijjani Hashim; Ɗandarman Kano, Alhaji Bello Bayero, da Kachallan Kano, Alhaji Magaji Galadima.
Waliyyan na amarya da ango sun yi zama a Gidan Gwamnatin Sakkwato, inda tsohon gwamnan jihar, Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa, ya bada amincewar baikon a madadin iyayen amarya.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, bai samu halarta ba amma Wazirin Sakkwato, Alhaji Sambo Junaidu, ya wakilce shi.
A wajen zaman, an biya sadakin A’isha lakadan N250,000. Yanzu ɗaurin aure da biki kawai su ka rage.