• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, May 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a ƙaddamar da sabon bugu na littafin tarihin Daular Usmaniyya a ranar Talata

by DAGA IRO MAMMAN
November 22, 2021
in Marubuta
0
Za a ƙaddamar da sabon bugu na littafin tarihin Daular Usmaniyya a ranar Talata
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A RANAR Talata, 23 ga Nuwamba, 2021, za a yi taron ƙaddamar da sabon bugu na wani sanannen littafin tarihin Daular Usmaniyya a garin Abuja.

Kamfanin Premium Times Books ne ya ɗauki nauyin fito da bugun Nijeriya na littafin mai suna ‘The Sokoto Caliphate’.

A sanarwar da mujallar Fim ta gani, masu shirya taron sun ce a Cibiyar Tunawa da Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja za a yi taron ƙaddamarwar, kuma Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamali, shi ne zai shugabanci taron.

Akwai ɗimbin manyan Nijeriya da aka gayyato. Sun haɗa da Ministan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare, wanda zai zama babban baƙo na musamman, yayin da Alhaji Nasiru Danu, shugaban kamfanin Casiva Limited, zai zama babban mai ƙaddamarwa.

Babban Editan jaridar’21st Century Chronicle’, Malam Mahmud Jega, shi ne zai gabatar da sharhi kan littafin, inda daga nan wasu zaɓaɓɓun mutane za su yi tattaunawa kan littafin a kan maudu’in muhimmancin tarihin Daular Usmaniyya ga Nijeriyar mu ta yau (wato “The Relevance of the History of the Sokoto Caliphate to Present-day Nigeria.”

Waɗanda aka zaɓa su yi tattaunawar a kan jigon su ne Farfesa Mukhtar Umar Bunza, Kwamishinan Ilimin Gaba da Firamare na Jihar Kebbi; da Farfesa Mohammed Junaid na Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto; da kuma shi Malam Jega.

Babban Janar Manajan Hulɗa da Jama’a na kamfanin man fetur na Nijeriya, wato NNPC, Mista Ohi Alegbe, shi ne mai tsawatarwa a lokacin tattaunawar. Hasali ma dai shi ne zai yi aikin sanƙira a taron.

Farfesa Murray Last

Tun a ranar 1 ga Nuwamba ne dai aka gudanar da ɗan ƙaramin bikin ƙaddamar da littafin a Sakkwato a wani sashe na bikin murnar zagayowar ranar da aka naɗa Alhaji Abubakar Sa’ad a matsayin Sarkin Musulmi na 13.

Shi dai wannan littafi mai taken ‘The Sokoto Caliphate’, kamfanin Longmans ne ya fara buga shi a tun a cikin 1967, sakamakon zurfin bincike da Farfesa Denis Murray Last ya yi a lokacin da ya ke ɗalibin digiri na uku (PhD) a Jami’ar Badun.

Jigon littafin shi ne Daular Usmaniyya da aka kafa a ƙarni na 19 miladiyya a ƙarƙashin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

An bayyana cewa a lokacin da ta ke kan ganiyar ta, wannan daula ta malala tun daga ƙasar Kamaru ta yau, ta yi yamma zuwa Burkina Faso, sannan daga arewa zuwa gabas tun daga Agadas har zuwa Ilori.

Turawan mulkin mallaka, musamman ‘yan Birtaniyya da Faransa, sun riƙa kiran yankin da sunan Daular Fulani.

Loading

Tags: book launchcolonialismMahmud JegaMurry LastNasiru DanuNNPCSarkin Zazzau Ahmed Nuhu BamalliShehu Musa Yar'Adua CentreShehu Usmanu DanfodioSokoto CaliphateSunday Dare
Previous Post

An yi wa babban ɗan Sarkin Kano da ɗiyar Ummarun Kwabo baiko a Sakkwato

Next Post

Aishatu Musa Dalil, ‘yar shekara 18, ta lashe gasar rubutu ta ‘Hikayata’ ta 2021

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Aishatu Musa Dalil, gwarzuwar gasar 'Hikayata' ta bana, riƙe da kambin ta a zaure taron karramawar

Aishatu Musa Dalil, 'yar shekara 18, ta lashe gasar rubutu ta 'Hikayata' ta 2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!