AISHATU Musa Dalil ta lashe gasar rubutun gajerun labaran ƙirƙira ta ‘Hikayata’ ta bana.
An bayyana haka ne a wani ƙwarya-ƙwaryan shagali wanda aka shirya a daren yau a ɗakin taro na Ladi Kwali da ke otal ɗin Sheraton da ke Abuja.
Gidan rediyon BBC Hausa ne ke shirya gasar a kowace shekara.
Aisha, wadda ke zaune a Kaduna amma ‘yar asalin Jihar Adamawa ce, ‘yar shekara 18, wanda hakan ya sa ta kasance marubuciya mafi ƙarancin shekaru tun da aka fara gasar shekaru shida da su ka gabata.
Ta zama zakara ne da gajeren labarin ta mai suna ‘Haƙƙi Na’, wanda jigon sa shi ne fyaɗe.
Nana Aicha Hamissou Abdoulaye, ‘yar shekara 27 da ta zo daga Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, ta zo ta biyu da gajeren labarin ta mai suna ‘Butulci’.
Zulaihat Alhassan, ‘yar shekara 29 da ta zo daga garin Kaduna amma ‘yar asalin Jihar Kebbi ce, ita ce ta zo ta uku da labarin ta mai taken ‘Rahmat’.
An ba gwarzuwar gasar kyautar tsabar kuɗi dalar Amurka dubu biyu ($2,000) da lambar yabo; an ba ta biyu dala dubu ɗaya ($1,000) da lambar yabo, sannan an ba ta uku dala ɗari biyar ($500) da lambar yabo.
Wannan shi ne karo na farko da wata marubuciya daga ƙasar waje ta samu nasara a gasar.
Taron ya samu halartar manyan baƙi da su ka haɗa da Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar, da uwargidan Gwamnan Jihar Kano, Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje (Goggo), da tsohon sanata Comrade Shehu Sani.
Akwai kuma ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati, ‘yan jarida, marubuta, da sauran jama’a daga sassa daban-daban na rayuwa.
Mutane da dama sun yi jawabi, ciki har da na shugabar alƙalan gasar a bana, Dakta Hauwa Bugaje ta Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, wadda ta bayyana tasirin rubutu a cikin al’umma da yadda aka samar da zakarun gasar ta bana.
Shi kuma shugaban Sashen Hausa na BBC, Malam Aliyu Abubakar Tanko, ya yi jawabin maraba tare da bayyana sadaukarwar da BBC Hausa ke da ita wajen amfani da soshiyal midiya don ƙara kusantar jama’a.
A jawabin, ya sanar da jama’a cewa nan gaba kaɗan BBC Hausa za ta buɗe shafi a manhajar nan ta TikTok a ƙoƙarin ta na faɗaɗa ayyukan ta a kafofin sada zumunta na zamani.
Haka kuma ya bayyana cewa shirye-shirye sun kankama wajen tsara gagarumin bikin cikar BBC Hausa shekaru 65 da kafuwa, har ya bada tabbacin cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ma zai halarta.
A nasa jawabin, Gwamna Badaru ya bayyana farin ciki kan yadda BBC ke shirya wannan gasa, ya ce hakan zai taimaka wajen bunƙasa harshen Hausa.
Ya yi la’akari da cewa tunda an ce alƙalami ya fi takobi kaifi, abin da BBC ke yi zai taimaka gaya wajen isar da saƙonnin Hausa ga sassan duniya.
Haka kuma ya ɗau alƙawarin cewa zai taimaka wa zakarun gasar ta bana su samu aiki da zaran sun kammala karatun su.
Ya ƙara da cewa shi da uwargidan gwamnan Kano za su haɗa kuɗi domin a ƙara wa zakarun gasar kyautar da BBC ta yi masu.
Ita kuma Dakta Hafsat Ganduje, ta gode wa Allah kan ayyukan da BBC Hausa ke yi.
Ta yi murna da ganin cewa Aicha daga Nijar ta samu wannan kyauta da kuma yadda ‘yan wasu ƙasashen su ka shiga gasar domin hakan shaida ce mai nuna faɗaɗar harshen Hausa a duniya.
Dakta Hafsat ta yi fatan cin wannan gasa zai kasance buɗin basira ga zakarun gasar.
Ta ce a shirye ta ke ta taimaka wa wannan tsari na haɓaka harshen Hausa.
Masu jawabai sun haɗa da Darakta-Janar na Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC), Alhaji Balarabe Shehu Illela, da takwaran sa na Hukumar Gidajen Rediyon Tarayya (FRCN), Dakta Mansur Liman, waɗanda dukkan su ma’aikatan BBC ne a da.
Yayin da Balarabe ya riƙa aiko wa BBC da rahotanni daga birnin Beijing na ƙasar Chaina, shi kuma Mansur ya taɓa shugabantar Sashen Hausa na BBC.
Su kuma zakarun gasar, an ba Aisha Musa Dalil dama ta ce wani abu a madadin su, inda ta yi godiya ga Allah da Gwamna Badaru da kuma ma’aikatan BBC Hausa saboda wannan karramawa da su ka samu.
Sai dai mujallar Fim ta lura da cewa a ƙarshe Aisha ta kasa ci gaba da magana saboda kukan murna da ya sarƙe ta.
Wani abu wanda ya ƙara ƙayatar da taron shi ne nishaɗantar da mahalarta da fitacciyar mawaƙiyar nan da ke tashe, Khairat Abdullahi, ta yi da waƙoƙin ta, ciki har da wata waƙa da ta yi wa BBC Hausa.
A ƙarshen taron, Haruna Shehu Tangaza na BBC ya yi jawabin godiya, sannan aka bada dama ga jama’a da su ɗebi abinci da abin sha da aka shirya da kan su.
Daga nan an ci gaba da ɗaukar hotuna da yin musabaha da juna har zuwa lokacin da aka fara watsewa.
Malam Ibrahim Isa ne ya yi aikin mai gabatarwa a taron, kuma an riƙa yaɗa yadda taron ke gudana kai-tsaye ga masu kallo a shafin BBC Hausa na Facebook.
Yanzu dai gwarzayen gasar ‘Hikayata’ na shekaru shida su ne kamar haka:
2021 – Aishatu Musa Dalil
2020 – Maryam Umar
2019 – Safiyya Ahmad
2018 – Safiyya Jibril Abubakar
2017 – Maimuna Sani Idris Beli
2016 – A’isha Mohammed Sabitu
An tashi daga taron na daren yau da misalin ƙarfe 10.
Masha Allah ina taya su murna Allah qara jagora amin