A GOBE Asabar, 27 ga Nuwamba, 2021 Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, za ta gudanar da zaɓen shugabannin ta.
A wata sanarwa da sakataren kwamitin zaɓen, Malam Rabi’u Koli, ya fitar a yau, ya ce, “Mu na sanar da dukkan membobi na MOPPAN na Kaduna da ƙungiyoyin fim na Kaduna cewa gobe da ƙarfe 10:00 na safe za a gudanar da ‘congress’, zaɓe da kuma yaɗa manufofi ‘yan takara kafin zaɓen.
“Za a gudanar da wannan zaɓe a ɗakin taro mai suna ‘Media Centre’ da ke Independence Way, Kaduna.
“Dukkan ‘yan takara za su halarci wurin zaɓen. Jami’an tsaron Jihar Kaduna, Hukumar Al’adu ta Jihar Kaduna, Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kaduna, da hukumar alƙalai.”
Haka nan kuma kwamitin zaɓen ya sanar da cewa dukkan waɗanda za su gudanar da wannan zaɓen daga kowace ƙungiya, kama daga ƙungiyar furodusoshi, daraktoci, ‘yan wasa, masu ɗaukar hoton bidiyo, editoci da sauran su kowa zai biya N1,000 na harajin shekara-shekara da ya kamata a ce ana biya, amma an ɗauki tsawon lokaci babu wanda ya ke biyan wannan haraji.
A gobe kafin masu kaɗa ƙuri’a su shiga ɗakin zaɓen kowa sai ya bada nasa harajin, amma an yafe wa kowa na shekarun baya da su biya ba.
Masu takarar zama shugaban ƙungiyar su ne Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj) wadda ta sauka kwanan nan bayan ta cika wa’adin farko na shekara huɗu, da kuma Alhaji Hamisu Jibrin Goma.
Tuni dai ‘yan takarar shugaban da na sauran muƙamai su ka jima su na yaƙin neman zaɓe a cikin membobin ƙungiyar.