• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda aka kashe jarumi Sani SK da labarin ƙarya a soshiyal midiya

by DAGA IRO MAMMAN
November 21, 2021
in Labarai
0
Sani Garba SK a asibiti, cikin wani bidiyo inda ya ke roƙon kuɗin magani

Sani Garba SK a asibiti, cikin wani bidiyo inda ya ke roƙon kuɗin magani

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A DAREN jiya wani mugun labari ya ɓarke a soshiyal midiya, aka ce wai fitaccen jarumi Sani Garba SK ya rasu.

Wasu gidajen yana da shafukan tattaunawa sun yaɗa labarin wanda ya bazu kamar wutar bazara. 

Labarin ya ɗaga hankalin mutane da dama, wasu na ta tambayar idan da gaske ne, yayin da wasu kuma sun gaskata shi.

Babu ruwan irin waɗannan shafukan da bin ƙa’idar aikin jarida ta tabbatar da labari kafin a buga shi, shi ya sa su ke rige-rigen yaɗa labarin ƙanzon kurege, abin da a Turance ake kira ‘fake news’.

Binciken da mujallar Fim ta yi ya gano cewa shafukan labarai da dama a Facebook sun yaɗa ƙirƙiri labarin, ko da yake daga baya wasu sun ƙaryata kan su da kan su.

Sai dai tun a lokacin da labarin ya ɓulla wakilan mu su ka gano cewa shaci-faɗi ne da ƙage.

‘Yan fim da dama sun nuna damuwa kan wannan labarin ƙaryar da aka yaɗa kan Sani SK, wanda ya ke kwance a Asibitin Nassarawa a Kano, ya na karɓar magani.

A makon jiya, a ranar 18 ga Nuwamba, an yaɗa wani guntun bidiyo a soshiyal midiya inda aka ga SK a zaune a kan gadon asibiti, ya na roƙon jama’a da su taimaka masa da kuɗin sayen magani.

Wani aminin majinyacin, fitaccen jarumi Aminu Surajo Bono, ya ɗauki saƙon murya da wayar sa bayan ya zanta da SK a daren jiya, ya tura wa jama’a tare da kira a gare su da su yi watsi da labarin da ake yaɗawa.

Aminu S. Bono ya ce: “Salamu alaikum jama’a. Don Allah duk wanda ya ke maganar S.K. ƙarya ne. Yanzu ma na kai minti biyar ina waya da shi, da wasan mu da dariyar mu yadda mu ka saba da kuma fara’ar sa da komai. Ya na nan a asibiti a ɗakin sa inda ya ke karɓar magani. 

“So, duk wanda zai ji wani abu a Facebook don Allah ya je ya yi ‘comment’ ya ƙaryata. Ƙarya ne!”

Mujallar Fim ta tuno da cewa ba a yanzu ba ne aka fara yaɗa labarin ƙarya kan mutuwar wani ɗan fim, domin kuwa tun ma kafin zuwan soshiyal midiya kusan kowane babban jarumi an sha cewa ya rasu.

Zuwan soshiyal midiya ya sanya irin wannan labarin ƙaryar ya fi saurin yaɗuwa, domin kuwa cikin minti kaɗan ya ke bazuwa a sassan duniya.

Jarumai biyu na baya-bayan nan da aka yi ƙaryar cewa ya rasu su ne Malam Sani Idris Kauru (Moɗa) da Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja Mazan Fama), waɗanda dukkan su mazauna Kaduna ne.

Loading

Tags: Aminu S. Bonofake newshausa filmsKannywoodmutuwaSamanjaSani Garba SKSani Idris ModaUsman Baba Pategi
Previous Post

Ni ɗan asalin Kano ne: Amsar Nuhu Abdullahi ga masu yi masa gorin asali

Next Post

An yi wa babban ɗan Sarkin Kano da ɗiyar Ummarun Kwabo baiko a Sakkwato

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Alhaji Kabiru Bayeto, babban ɗan Sarkin Kano

An yi wa babban ɗan Sarkin Kano da ɗiyar Ummarun Kwabo baiko a Sakkwato

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!