* Ya baje-kolin takardun sa a Facebook
TAURARON Kannywood Nuhu Abdullahi ya maida wa masu yi yarfen asali martani, inda ya nuna cewa shi cikakken ɗan Kano ne.
Don tabbatar da hakan, Nuhu ya baje-kolin takardun sa na makaranta da shaidar haihuwa.
Takardun sun haɗa da na shaidar makarantun firamare da sakandare da ya yi.
Nuhu, wanda ake yi wa laƙabi da Mahmoud, ya yi haka ne bayan wani mutum ya yi masa gorin asali sakamakon wata hira da sashen Hausa na BBC su ka yi da shi a shirin su na ‘Daga Bakin Mai Ita’.
Sun yi hira da Nuhu ne dangane da rayuwar sa da sana’ar sa ta fim.

Tun da farko mutumin, mai suna Ishaƙa Usman Wali, ya yi wa jarumin ƙorafi a kan yadda wai ya ke gudun asalin sa a dalilin ɗaukakar da ya samu.
A cikin buɗaɗɗiyar wasiƙar ta Ishaƙa, wadda ta bazu a soshiyal midiya, ya ce masa, “Na yi matuƙar mamaki irin yadda na kalli hirar ka da BBC Hausa a shirin su na ‘Daga Bakin Mai Ita’, inda su ka so su ji tarihin ka, kai kuma sai ka nuna masu cewa an haife ka a garin Kano, ka yi firamare da sakandare duk a Jihar Kano.
“Hakika na ji babu daɗi sakamakon irin yadda na ga ka juya wa ƙauyen ku baya saboda yanzu rayuwar ka ta ci gaba kuma na yi mamaki matuƙa.”
Da alama, wannan iƙirarin ya fusata jarumin a yau, mako guda bayan an yi hirar da shi, har ya baje-kolin takardun sa da ke nuna cewa shi haifaffen unguwar Kawo ne da ke yankin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a birnin Kano.
Sai dai kuma mujallar Fim ta lura da cewa jarumin ya yi wuf ya goge takardun da ya wallafa masu nuna asalin shi haifaffen Kano ne.
Sai dai daga baya jarumin ya yi wata gajeruwar nasiha ga matasa a kan su guje wa munanan halaye tare da ƙaurace wa dukkan abin da ka iya ɓata masu lokaci.
Ya ce, “Salam, kira na ga ‘yan’uwa na matasa mu maida hankali wurin ciyar da kan mu da wasun mu gaba, mu daina ɓata lokaci a kan abin da zai ɓata mana lokaci wanda bai da amfani.
“A ‘yan shekaru na na samu cigaban da ko a mafarki ban yi zaton zan samu ba, amma Allah cikin ikon sa ya sa na samu.
“Mu zama masu jajircewa a kan abin da ya ke gaskiya da kuma amana. Mu kuma guji ƙarya da sharri da hassada da ƙyashi, Allah sai ya taimake mu.
“Wanda ya yi min waccan ƙaryar na yafe masa, kuma Allah ya shiryar da shi, amin.”
Gorin asali dai ba baƙon abu ba ne ga mutanen da su ka yi shuhura a wani ɓangare na rayuwa. Sai dai kuma a mafi yawan lokuta a birnin Kano a kan yi wa mutum gorin cewa ba ɗan asalin garin ba ne, inda a kan jefe shi da kalmar ‘baƙo’ ne ko kuma a danganta da shi da wata ƙabila ta daban.
![]()







